LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bauchi: 'Yan sanda sun kama matashi da ya lalata kaninsaRundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta damke Yusuf Saleh mai shekaru 36 sakamakon zarginsa da ake da yin luwadi sa kaninsa. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ahmed Wakili, wanda ya bayyana hakan a wata takarda, ya ce an kai musu rahoton al'amarin a ranar 5 ga watan Afirilun 2020.

Kuma mahaifin yaran ne ya kai rahoton. Ya ce Saleh ya ja kaninsa zuwa wani kango inda ya yi lalata da shi ta baya. DSP Wakili ya kara da cewa, wanda ake zargin ya siyawa wanda ya lalata biskiti da lemun kwalba don toshe masa baki.

Ya ce, "A ranar 5 ga watan Afirilun 2020 wurin karfe 9:26 na dare wani Ibrahim Umar da ke Makama New Extension Federal Low-cost Bauchi ya kai rahoto ofishin 'yan sanda. "Ya ce wurin karfe 7:30 na yammacin ranar wani Yusuf Saleh mai shekaru 36 da ke yankin Zango a Bauchi ya yaudari kaninsa zuwa wani kango tare da lalata shi ta karfin tsiya.

"Daga nan ya siya masa lemun kwalba tare da biskiti. Bayan nan, an kama Saleh kuma ya amsa laifinsa." Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce wasu jami'ai sun damke kungiyar 'yan fashi da makami da suka addabi Bauchi, Taraba da Adamawa. Ya ce an kama tara daga ciki masu alaka da fashi da makamin da ya addabi jihohin.

Kamar yadda yace, 'yan fashin sun amsa cewa sun dade suna aika-aikar kuma su ke fashin ababen hawa a jihohin uku tare da siyar da su a kasashen Kamaru da Nijar. Wakili yace, "A ranar 12 ga watan Yunin 2020 wurin karfe 10:03 na yamma, mun samu kira daga wani Abdullahi da ke Agric Quarter da ke Tirwun a kan titin Maiduguri. Ya ce 'yan fashi sun tsare shi a gidansa. "Bayan karbar motarsa Honda CRV, katin ATM da sauransu,

sun tirsasa shi bada lambar katinsa inda suka zare N120,000 daga asusun bankinsa. "Bayan samun wannan bayani, jami'ai sun gaggauta zuwa inda suka damke takwas daga ciki."KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments