--
Da dumi dumi: An sake kai hari jihar Zamfara, rayukan mutane 10 sun salwanta

Da dumi dumi: An sake kai hari jihar Zamfara, rayukan mutane 10 sun salwanta

Wasu 'yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara, inda suka kashe akalla mutum goma tare da sace shanu da dama. Wannan sabon hari ya auku ne a garin Ruwan-Tofa na gundumar Dansadau da ke karkashin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara. Har wa yau, Maru da Talata Mafara, su ne kananan hukumomin, da 'yan bindiga suka kai munanan hare-hare a ranakun 2 da kuma 3 ga watan Yuni,

inda suka kashe mutum 21. Hukumar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar wannan sabon hari kamar yadda karidar Premium Times ta wallafa. A yayin da ya ke ganawa da manema labarai, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Muhammad Shehu, ya ce rayukan mutane 10 sun salwanta a sabon harin da yan bindiga suka kai. Ya kuma bayar da shaidar cewa, hukumomin tsaro tare da gwamnatin jihar na ci gaba da fadi-tashin ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali sun wanzu a jihar.

Mazauna garin Ruwan-Tofa sun ce maharan da suka kawo harin haye a kan babura fiye da 110 sun kai akalla 200, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi. Wadanda suka ba da shaidar da suka bukaci a sakaya sunayensu saboda dalilai na tsaru, sun kuma ce maharan sun kuma yi awon gaba da dabbobin kiwo da dama.

Sun ce: "Harin ya auku ne da misalin karfe 6.00 na Yammacin ranar Asabar." "Babu wata tangarda da 'yan bindigar suka fuskanta daga jami'an tsaro yayin da suke cin karensu babu babbaka." Bayan tarzoma ta lafa, an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin Dansadau," inji wani mazaunin garin."Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su sun karasa cikawa a asibitin." An ruwaito cewa,

wannan sabon hari ya auku ne 'yan awanni kadan bayan da 'yan sanda a jihar Zamfara suka yi alkawarin inganta tsaro a karamar hukumar Maru da sauran sassa na jihar. A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, 'dan bindiga daya ne ya rasa ransa yayin da wasu da yawa suka jikkata bayan da dakarun soji suka kai simame maboyarsu a jihar Binuwai. Shugaban fannin yada labarai na hedikwatar tsaro,

John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda da ya bai wa manema labarai a ranar Lahadi. Ya ce an kai simamen ne a ranar Asabar kuma dakarun sun yi nasarar tarwatsa maboyar 'yan bindigar tare da samun makamai.

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Da dumi dumi: An sake kai hari jihar Zamfara, rayukan mutane 10 sun salwanta"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?