--
Zargin damfara: APC ta bukaci gwamnan Bauchi ya yi murabus ko a tsigesa

Zargin damfara: APC ta bukaci gwamnan Bauchi ya yi murabus ko a tsigesa

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bauchi, ta ce rahotannin kwace kadarar gwamnan Bala Mohammed ta miliyoyin naira da ICPC tayi ya isa ya zama hujjar da za ta sa ya yi murabus a matsayin gwamnan jihar ko a tsigesa. Idan za mu tuna, an kwace kadararsa ta Zinaria International School wacce ke fuloti na 298 da ke yankin Wuye, Cadastral Zone B3 a birnin tarayya.

A yayin tabbatar da kwace ginin, kakakin hukumar ICPC, Rasheedat Okoduwa ta ce ba za su iya gurfanar da Mohammed ba saboda kariyar da yake da ita kamar yadda sashi na 308 na kundun tsarin mulki ya bayyana. Hukumar ta sanar da cewa za ta gurfanar da gwamnan ne bayan ya kare wa'adin mulkinsa.

Amma jam'iyyar APC ta yi kira ga gwamnan da ya sauka daga mulkin jihar a mutunce. Wannan bukatar na kunshe ne a wata takarda da jaridar The Nation ta samu bayan shugaban kwamitin yada labarai na jam'iyyar APC a jihar, Kwamared Sabo Mohammed da sakatare Mallam Sa'adu Umar suka sa hannu. "APC ta gano handamar da gwamna Bala Mohammed yayi na wata kadara wacce ICPC ta kwace a Abuja.

"Kakakin hukumar ICPC ta ce Gwamna Bala Mohammed ya samu dukiyar ne ba ta yadda ya dace ba kuma mallakin ma'aikatar noma da kiwo ce. "Wannan wawurar za ta iya bada damar ya sauka daga mulki ko a tsigesa. A don haka muke kira gareshi da ya bi hanyar da ta dace a mutunce," takardar tace. Amma a martanin gaggawa da gidan gwamnatin jihar ya fitar, ya musanta rahoton hukumar wanda ta ce labaran kanzon kurege hukumar ke fadi a kan gwamnan.

A baya mun ji cewa hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) a ranar Talata, 16 ga watan Yuni, ta sanar da kwace wani gini mallakin Sanata Bala Muhammad wanda ya same shi a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya Abuja. Ginin ne Zinaria International School da ke fuloti 298, yankin Wuye, Cadastral Zone B3 Abuja. Kamar yadda takardar ta bayyana a shafin hukumar ta Twitter, ta ce bincike ya nuna cewa Sanata Mohammed ya mika ginin makarantar ga hukumar a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya.


 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Zargin damfara: APC ta bukaci gwamnan Bauchi ya yi murabus ko a tsigesa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?