--
Naira ta yi kasa war-was a kasuwar canji, Dalar Amurka ta lula ta haura N450

Naira ta yi kasa war-was a kasuwar canji, Dalar Amurka ta lula ta haura N450



A ranar Laraba, 18 ga watan Yuni, 2020, an saida Dalar Amurka a kan N452 a kasuwar canji a Najeriya. Hakan ya zo ne bayan wasu rade-radi da ke yawo a kasuwar kasar. Jaridar Punch ta bayyana cewa bashin kasar wajen da ke kan gwamnatin Najeriya ya na cikin abubuwan da su ka yi sanadiyyar karyewar Naira a cikin farkon makon nan.

Babban bankin Najeriya ya dawo da saidawa bankunan kasuwa Dala a cikin watan Afrilu domin masu bukatar biyan kudin makaranta a kasashen waje da kuma shigo da kaya. Kafin wannan lokaci bankin na CBN ya dakatar da saida Dala ga masu shigo da kaya Najeriya daga ketare.

Masu harkar sun shaidawa Jaridar Punch cewa wannan ya kawo matsala. Shugaban ‘yan kasuwar canji a Najeriya, Alhaji Aminu Gwadabe ya ce dakatar da saidawa bankuna Dala ya jawo matsala a kasuwa, inda rade-radin da ake yi su ka jawo tashin farashi.

Aminu Gwadabe ya ke cewa: “Mutane su na amfani da wannan dama ganin cewa yanzu bashin kudin kasar waje ne hanyar samun kudin shigan Najeriya ba mai ba.” “Akwai bukatar bankin CBN da kwamitin yaki da annobar cutar COVID-19 su sa ido a kan mugun aikin da ‘yan kasuwar canji su ke yi, domin a ceci kudin Najeriya.”


“Tattalin arzikinmu ya dogara ne sosai da tufafi, mai, abinci, kayan asibti da sauran kaya da ake shigo da su daga kasar waje.” Inji Gwadabe. Gwadabe ya kuma bayyana cewa akwai bukatar a nemi wasu hanyoyin samun Dala a Najeriya. Daga cikin wadannan hanyoyi akwai aiko kudin kasar waje Najeriya daga ketare. Shugaban ‘yan canjin ya kara da cewa: “Dala ta koma N452/$ yau (Laraba) a kasuwa, kuma farashin na cigaba da tashi ne, abin na da ban tsoro muddin BDC ba su dawo aiki ba.”


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Naira ta yi kasa war-was a kasuwar canji, Dalar Amurka ta lula ta haura N450 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?