--
Zargin Malamin addini da fyade: Kotu ta yi watsi da karar

Zargin Malamin addini da fyade: Kotu ta yi watsi da karar



Wata kotun majistare da ke Ede a jihar Osun, ta yi watsi da karar wani malamin addinin Musulunci mai suna Habeebulah Abdulrahman wanda ake zargi da yi wa matashiya mai shekaru 16 fyade. Alkalin kotun, A. Oluwolagba, ya ce hukuncin ya biyo bayan shawarar sashen gabatar da kararraki na ma'aikatar shari'ar jihar.

Wadanda suka samu halartar kotun sun sanar da Premium Times cewa hukuncin ya kawo rikici da muhawara tsakanin alkalin da mai gabatar da karar wanda ya fusata da hukuncin. Kamar yadda mai gabatar da kara, Adepoju Sunday ya bayyana, DPP ta dogara da rashin takardar shaida daga likita a kan fyaden da malamin yayi.

"Sashen bincike na jihar ya kammala bincike kuma malamin ya amsa cewa ya yi lalata da yarinyar har sau biyu. Amma mun gano cewa daga sama ne shawarar ta zo," ya sanar da jaridar a tattaunawar da akayi da shi a ranar Alhamis. Wasu 'yan uwan wacce al'amarin ya faru da ita sun zanta da Premium Times bayan hukuncin a ranar Laraba. Sun jajanta rashin adalcin da aka yi musu a bayyane.

Lauyan wacce aka yi wa fyaden, Abdulrasheed Maisolati ya nuna mamakinsa a kan hukuncin kotun. Maisolanti, wanda bai samu damar zuwa kotun ba a ranar Laraba saboda hana zirga-zirga da aka yi, ya ce ya san kotun za ta yanke hukunci a ranar. Amma a lokacin rubuta wannan rahoton, bai sanar da matakin gaba da za su dauka ba. Uloma Obike-Adim, shugaba a kungiyar Amnesty International, ya ce tuni suka fara kokarin kalubalantar hukuncin kotun.

Obike ta jajanta hauhawar rahotannin fyaden da ke yawo a kasar na. Ta ce fannin shari'a basu taimakawa wurin daukar mataki. "Tuni muka fara zargin cibiyoyin tsaro amma fannin shari'a abun takaici ne," tace a ranar Alhamis.

Amma kuma, da aka tuntubi fannin shari'a a kan bayani, jami'in yada labarai na ma'aikatar shari'a, Opeyemi Bello ya ce bai san da shari'ar ba. Ya yi alkawarin tuntubar manema labarai idan ya samu gamsassun bayanai daga ma'aikatar.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Zargin Malamin addini da fyade: Kotu ta yi watsi da karar"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?