--

EFCC: Zai yi shekaru 16 a gidan yari bisa laifin damfarar wasu Mata N780, 000

EFCC: Zai yi shekaru 16 a gidan yari bisa laifin damfarar wasu Mata N780, 000



Kotu ta daure wani mutumi mai suna Ramat Mohammed bayan an same shi da laifin damfarar zaurawa 194. Ramat Mohammed wanda aka fi sani da Gaddafi, zai shafe shekaru 16 a gidan kurkuku. A ranar Talata, 16 ga watan Yuni, 2020, Alkali Umaru Fadawu na babban kotun tarayya da ke Borno, ya kama Ramat Mohammed da laifin damfarar wadannan Bayin Allah, ya karbe masu N781, 000, 000.

Kamar yadda hukumar EFCC ta bayyana, Ramat Mohammed ya yi aiki a matsayin malamin shari’a a gwamnatin jihar Borno. Alkali ya samu wannan mutumi ne da laiffuka biyu na damfara da sata. Mohammed ya yi amfani da sunan wani mutumi inda ya rika saidawa mata wani kati da sunan kungiyar NGO mai zaman kanta.

Wannan mutumi ya saida katin rabon abinci da sunan kungiyar Action Against Hunger, inda aka haka ya tara N781, 800, 000 daga hannun zaurawa kusan 200. A karshe dubunsa ta cika, yayin da EFCC ta yi ram da shi.

Mata 40 da aka nemi a damfara su na karatu ne a wata makarantar islamiyya mai suna Fissabi-lillah da ke garin Auno a cikin karamar hukumar Konduga, jihar Borno. Wannan aiki da Ramat Mohammed ya yi ya ci karo da sashe na 1(1)a na dokar damfara da sata na shekarar 2006. A lokacin da aka karanta masa laifinsa, wanda ake zargin ya amsa cewa bai da gaskiya.

A dalilin haka ne Alkali Umaru Fadawu ya yanke masa hukuncin daurin shekara takwas na kowane daga cikin laifin. Alkalin ya ce shekarun zaman kason za su yi aiki ne a lokaci guda. Kotu ta kuma bukaci wanda aka kama ya biya wadannan matan islamiyya kudinsu har N781, 800.00



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "EFCC: Zai yi shekaru 16 a gidan yari bisa laifin damfarar wasu Mata N780, 000"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?