--
'Mun fara binciken bidiyon 'yan sanda masu POS'

'Mun fara binciken bidiyon 'yan sanda masu POS'



Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kaddamar da bincike domin gano sahihancin wani bidiyo da ya nuna yadda wasu jami'an 'yan sanda ke amfani da na'urar cirar kudi ta POS wajen karbar cin hanci da ga jama'ar gari.

Rundunar ta bukaci duk wani mai bayanai da ya taimaka su tuntube ta ta shafinta na pressforabuja@police.gov.ng

Babban sufeton 'yan sandan kasar ya yi tur da karbar cin hanci a tsakanin ma'aikatan gwamnati musamman 'yan sanda.

Ya kuma ce rundunar a shirye take ta hukunta duk wani jami'i da aka samu da hannu a cin hanci da rashawa.

Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan da wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wasu 'yan sanda a shingen da suka kafa a kan titi na amfani da na'urar cire kudi ta POS domin karbar na goro.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "'Mun fara binciken bidiyon 'yan sanda masu POS'"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?