LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga a wasu kananan hukumomi
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga har tsawon sa’o I 24 a kananan hukumomin Zangon Kataf da garin Chawai da ke karamar hukumar Kauru.

Gwamnatin ta kuma ce dokar za ta fara aiki ne nan take.

Wannan na cikin wata sanarwa da kwamishinan harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya fitar a ranar Alhamis.

A cikin sanarwar Samuel Aruwan ya ce hukumomin tsaro suna kokarin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi yankunan a yanzu haka.

A makon da ya gabata ne aka samu barkewar rikici a Zangon-Kataf a kan wata gona, lamarin da ya haifar da fargaba a zukatan mazauna yankin.

A cewar kwamishinan, shugabannin al’ummar yankin sunyi kokarin shawo kan matsalar, sai dai hakan ya gagara, lamarin da ya sanya gwamnatin jihar daukar matakin hana zirga-zirga.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments