--
Majalisar Dinkin Duniya za ta ba Najeriya $180m domin yaki da COVID-19 da yunwa

Majalisar Dinkin Duniya za ta ba Najeriya $180m domin yaki da COVID-19 da yunwa

ROHOTON: LEGIT.NG


UN za ta taimakawa Jihohin Arewa maso Gabas da rikicin Boko Haram ya ci  Haka zalika za a tallafawa Kano, Legas da Abuja inda COVID-19 ta yi kamari

Mutum akalla 8, 000 ne Coronavirus ta harba tsakanin Kano, Legas da Abuja

Jaridar The Guardian ta ce Majalisar dinkin Duniya ta na kokarin hadawa miliyoyin mutanen Najeriya da annobar cutar COVID-19 ta shafa gudumuwa na musamman.

Majalisar dunkin Duniyar za kuma ta bada agaji ga mutanen yankin Arewa maso gabas da su ke cikin wani mawuyacin hali a sakamakon yakin Boko Haram da ake ta yi.

Hukumar Duniyar za ta taimakawa Najeriya ne da fam Dala miliyan 182. Idan aka yi lissafi a kudinmu na gida, wannan gudumuwa za ta kai kimanin Naira biliyan 70.3.

A cewar hukumar WFP, wadannan makudan kudi za su yi amfani na tsawon watanni shida ana ba ‘yan Najeriyar da wannan annobar cuta da kuma matsalar tsaro ta shafa.

Mutane miliyan uku da ke yankin Kano, Abuja, da Legas za a kawowa dauki da wannan kudi, baya da irin kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi a manyan biranen kasar.

Mai magana da yawun bakin hukumar WFP ta Duniya, Elisabeth Byrs, ta koka da yadda mutanen yankin Borno, Yobe da kuma Adamawa su ke fama da yunwa a halin yanzu.


Wadannan jihohi uku su ne inda rikicin ta’addancin Boko Haram ya fi yi wa tasiri a Najeriya.

A wani jawabi da Elisabeth Byrs ta fitar a ranar Laraba, 10 ga watan Yuni, 2020, ta ambaci wadannan jihohi a matsayin inda su ka fi bukatar taimako a yankin Tafkin Chadi.

Akwai mata da kananan yara fiye da miliyan 7.9 da su ke matukar bukatar agaji.

Legas, Kano da Abuja kuma su ne jihohin da aka fi samun barkewar cutar Coronavirus. Akwai fiye da mutane 8, 300 da su ka kamu da COVID-19 kawo yanzu a wadannan garuruwa.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Majalisar Dinkin Duniya za ta ba Najeriya $180m domin yaki da COVID-19 da yunwa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?