LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kisan Qasseem soleimani: Iran ta ba da sanarwar kama Donald TrumpMARIGAYI SHAHEED QASEEM SOLEIMANI KWAMANDAN SOJI NA MUSAMMAN A IRAN 
Iran ta bayar da sanarwar kama shugaban Amurka Donald Trump kan kisan babban kwamandanta Janaral Qassem Soleimani.

Hukumomin Iran sun ce Mista Trump da wasu mutane sama da 30 za su fuskanci tuhumar kisan kai da kuma ta'addanci, sun kuma nemi agajin 'yan sandan kasa da kasa a shari'ar.

An kashe Janaral Soleimani a wani harin sama da dakarun Amurka suka kai Baghdad babban birnin kasar a watan Janairu.

Masu sharhi sun ce umarnin kamun kawai wata magana ce ta fatar baki wadda ba za ta yi tasiri ba, sai dai yana nuna wata tsantsar kiyayyar da shugabancin Iran ke yi wa Donald Trump.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments