LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Sama da mutum miliyan 1 ne suka cika aikin N-Power cikin awa 48

Cikin abinda bai fi kasa da awa 48 ba da bude shafin yanar gizo na N-Power domin mutane suyi rijista, sama da mutane miliyan daya sun cika aikin, a cewar wata sanarwa ta musamman.

Ma’aikatar jin kai da walwalar jama’a ta kasa, ita ce ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi da daddare.

“Ma’aikatar jin kai da walwalar jama’a tana sanar da cewa sama da mutum miliyan daya sun cika aikin N-Power a fadin Najeriya cikin awa 48, bayan mai girma minista, Sadiya Umar Farouq, ta sanar da bude shafin yanar gizo na N-Power din.

“Ma’aikatar tana so ta kara tabbatarwa da matasan Najeriya da suke tsakanin shekara 18-35 da suke da ilimi ko babu cewa za su iya cika wanna tsari da zai fi bayar da karfi a fannin noma.

“Yawan mutanen da muka samu yanzu, yana nuni da yawan matasan da suke bukatar aiki kuma suke da tabbaci akan wannan tsari.

“Ma’aikatar za ta cigaba da aiki da ma’aikatan ta dan bayar da taimako ga duka mutanen da suka cika,” cewar sanarwar.

Ma’aikatar ta sanarwa da ‘yan Najeriya a cikin sanarwar cewa za ayi adalci wajen zabar wadanda suka samu nasara, sannan za a nunawa kowa ya gani.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments