LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Da dumi duminsa: Kotu ta yanke hukunci kan kisan yan' shi'a 3 yan sanda zasu biya diyya

Daga Aljaafaree Kaduna: 


Babbar kotun tarayya dake Abuja ta yanke Hukunci mai tsanani ga hukumar 'Yan sandan Najeria inda Alkalin Kotu mai lamba ta tara (Court 9) Justice Taiwo O. Taiwo ya yanke Hukuncin cewa
(a) Kisan da 'Yan sanda suka yi ya saba dokar kasa wato sunyi kisan ba bisa ka'ida ba.


(b) Su biya diyyar Naira Miliyan biyar (5,000,000) ga ko wane mutum daya da suka kashe.
(c) Su bada gawawwakin ga iyalan mamatan.

Idan ba'a manta ba yau 29 /06 /2020 ne za'a yanke Hukunci na mutane uku cikin yan shi'a shida da 'Yan sanda suka kashe ranar Litini 22 July 2019 a kofar Majalisar kasa sakamakon zanga-zangar da sukayi ta neman Gwamnatin tarayya ta saki Jagoran su Sheikh Ibraheem  El-Zakzaky.


Sun kashe Mutane da yawa an iya dauka 6 a ranar sun tafi da 3 (wadanda aka yanke Hukuncin su yau)
Wasu sun karasa a hannun yan sanda.Wadan da aka yanke Hukuncin akan su yau sune
1. Shahid Suleiman Shehu Darki Kano
2. Shahid Mahdi Musa Zaria
3. Shahid Bilyaminu Abubakar Faska


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments