LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Da kanta take zuwa dakina da daddare tace nayi lalata da ita – Cewar mutumin da ya yiwa diyarshi mai shekaru 13 fyadeA ranar Juma’ar nan ne, rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kama wasu masu fyade guda biyar, ciki hadda wani mai shekaru 50, mai suna Adeleye Fayemiwo, wanda ya yiwa ‘yarshi mai shekaru 13 fyade.

Da yake magana da manema labarai, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mr Undie Adie, ya ce Fayemiwo da sauran masu laifin guda hudu duka an kama su sakamakon kararsu da aka kawo ta yiwa mutane fyade.

Kwamishinan ya ce wani dan shekara 28 mai suna Oyerinde Oyeniyi, dake yankin Mokuro, a karamar hukumar Ile-Ife, an kama shi da laifin yiwa diyar mai gidan da yake haya a gidanshi, wacce ke da shekaru 11 a duniya.

Adie, wanda ya nuna rashin jin dadinsa akan cigaba da samun yawaitar fyade da ake yi a jihar, ya ce, “Wani mai suna Isiaka Adeyounbo dake a Ayelabowo Street, Ile-Ife, ya ja wata yarinyar mai shekaru 16 zuwa gidanshi, inda yayi lalata da ita.

“Bayan karbar kararraki, an kama masu laifin, inda wadanda aka yiwa fyaden kuma aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

“Wani mai suna Eronse Balat daga Eleyele, Ile-Ife, shi ma an kama shi da da laifin yiwa ‘yar uwarshi mai shekaru 23 fyade.

“Fayemiwo ya amsa laifinsa na yin lalata da ‘yarsa, amma yace ya aikata laifin ne a lokacin da yasha giya ya bugu, sannan ya roki ayi masa afuwa.

Ya ce, “Ni manomi ne yarinyar kuma ‘yata ce. Na ce mata ta dafa mini abinci taki yi. Tana zuwa dakina ta dinga rokona akan nayi lalata da ita. Ranar dana kwanta da ita, na sha giya ne. Na yi lalata da ita ne a lokacin da nake buge. Mahaifiyarta mun rabu. Ina da mata, amma ita wannan yarinyar kullum sai ta zo da daddare ta nemi nayi lalata da ita.”


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments