--
Da dumi duminsa: An samu man fetur a jihar Filato

Da dumi duminsa: An samu man fetur a jihar Filato


ROHOTON: LEGIT.NG


Sabuwar sanarwa da kamfani man fetur na Najeriya (NNPC) ta fitar ya bayyana cewa an samu man fetur a jihar Filato da ke Arewacin Najeriya.

An samu albarkar man fetur a jihohin Borno, Bauchi, Gombe da Niger da ke Arewacin Najeriya. Hakan zai taka rawar gani wurin habbaka tattalin arzikin Najeriya.

Cike da jin dadi kwararru tare da shugabannin yankin ke bada shawarar yadda za a amfana da wannan albarkar kasar da ke jihar don samun ci gaba.

NNPC ta ce an fara kokarin fitar da man fetur da iskar gas a kananan hukumomin Wase da Kanam na jihar Filato.

An gano cewa Wase da Kanam, na da makwabtaka da Binuwai kuma suna da yawan man fetur da iskar gas da za ta iya tallafawa tattalin arzikin kasar nan.

A yayin ziyarar da kamfanin man fetur ta kai gidan gwamnatin jihar wurin Gwamna Simon Bako Lalong, manajan daraktan kamfanin, Mele Kyari, ta bakin manajan hakar man fetur, Abdullahi Bomai, ya ce kamfanin ya gano man fetur a inda suke kira Kolmani.

Baya ga yankin Neja Delta, an samu gangar man fetur biliyoyi a yankin.

Da suka je duba yankunan a jihar Filato, Daily Trust a ranar Lahadi ta gano cewa kungiyar ta duba yankunan Kanam da Wase ina ta yi shaida a yankunan da za a fara aiki.

A kalla nisan kilomita 70 daga wurin da za a yi aikin a Wase, NNPC ta fara ginawa ma'aikata sansani wadanda za su fara aikin duba yankin.

Kamfanin ya zuba kwantenoni wadanda za su zama ofisoshin ma'aikatan na wucin gadi, janareto don wutar lantarki da sauran kayayyakin aiki duk an kaisu yankin.

Sarkin Yuli, Alhaji Yaro Shu'aibu, wanda yayi magana a kan aikin, ya ce jama'ar yankin sun yi matukar farin ciki ganin cewa NNPC za ta hako man fetur a yankin. Ya yi alkawarin bada hadin kai domin samun nasarar aikin.

"Jama'ar yankin nan suna farin ciki kuma muna fatan za a kammala aikin nan babu dadewa. Muna farin cikin zama yankin da zai bada gudumawa a kasar nan," yace.

Hakazalika, daya daga cikin masu nada sarakuna a Kukawa da ke Kanam, Hassan Salisu Muhammad, ya ce gano man fetur a yankin ci gaba ne mai kyau ga dukkan yankin.

"Da tsananin farin ciki muke godiya ga Ubangiji. Muna farin cikin abinda muke ji a wasu kasashe da wasu sassan kasar nan mun samu a gidanmu. Muna fatan gwamnati za ta bada goyon bayan wurin samun nasarar ayyukan," yace.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Da dumi duminsa: An samu man fetur a jihar Filato"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?