LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

COVID-19: 'Yan sanda sun rufe hanyoyin shiga unguwar su Shehu Sani a Kaduna

'Yan sanda a jihar Kaduna sun datse hanyoyin shiga layin su Sanata Shehu Sani a unguwar Sarki Kaduna - 'Yan sandan sun rufe hanyoyin shiga layin ne sakamakon rasuwar wani fitaccen dan kasuwa da ke gida a layin

Ana zargin cewa cutar coronavirus ce ta yi sanadin mutuwar dan kasuwar mai suna Shehu Usman Jami'an Rundunar 'Yan sanda a jihar Kaduna sun rufe Layin Ahman Pategi daura da Abbas Road a unguwar Sarki Kaduna bayan wani fitaccen dan kasuwa Shehu Usman ya rasu sakamakon rashin lafiya da ake zargin coronavirus ce.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa gawar marigayin tana nan a asibitin Saint Gerald da ke Kaduna kuma har yanzu ba a bawa iyalansa gawar ba.

Wakilin majiyar Legit.ng kuma ya ruwaito cewa a kalla yan sanda 12 sun rufe hanyoyin shiga layin da gidan dan kasuwar ya ke. An gano cewar a layin akwai gidajen manyan mutane da suka hada da Sanata Shehu Sani, Umaru Mutallab, Mahe Dange, jigo a jamiyyar D kuma dan takarar kujerar sanata a jihar Sokoto. Har wa yau, wani babban dan kasuwa, Mahdi Shehu, Mai Dialogue plaza, shima yana da gida a layin.

A wani labarin, kun ji cewa an birne gawar tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi a ranar Lahadi a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo. An yi wa Ajimobi jana'iza irin ta koyarwar addinin musulunci sannan aka birne shi a gidansa da ke 6th Avenue, Yemoja Street, Oluyole Estate, Ibadan cikin yanayi na tsaro kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnatin jihar ta Oyo ta ki amincewa a birne marigayin a gidansa da ke Agodi GRA saboda ana shariar a kotu game da gidan duk da cewa nan iyalansa suka fi so. An birne tsohon shugaban riko na jami'yyar All Progressives Congress, APC, mai mulki misalin karfe 10:05 na safe.

Ajimobi, mai shekaru 7 a duniya ya rasu ne a wani asibiti da ke Legas. Rahotanni sun ce an bi dukkan dokokin birne wadanda suka mutu sakamakon cutar coronavirus yayin janai'zarsa. Mutanen da suka hallarci jana'izar ba su kai 2 ba cikinsu har da matar tsohon gwamnan, Cif Florence Ajimobi da wasu daga cikin iyalansa na yan uwansa na kusa.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments