--
An yanke wa biri hukuncin ɗaurin rai da rai saboda kai wa mutane 250 hari

An yanke wa biri hukuncin ɗaurin rai da rai saboda kai wa mutane 250 hari



An yankewa wani bugaggen Biri dan giya hukuncin daurin rai da rai sakamakon dabi'ar rigima da ya bayyana bayan an hana shi 'abun sha'. Bugaggen Birin mai suna Kalua ya fada cikin mutum 250 inda ya tarwatsa su tare da kashe mutum daya har lahira.

A cikin wannan makon, masu kula da gidan namun daji da ke Kanpur sun tabbatar da cewa Birin babban hatsari ne ga sauran 'yan uwansa kuma an yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Birin da ya saba shan giyar mallakar wani likitan ido ne da ke yankin Mirzapur mai suna Uttar Pradesh, wanda makwabtansa suka tabbatar da cewa shi ya koya masa shan giya da cin naman Birai 'yan uwansa,

jaridar Daily Mail ta ruwaito. A lokacin da aka samu gawar mamallakin Birin, fusattacciyar dabbar ta fada titi inda ta dinga kaiwa da kawowa tana harar jama'a. Birin ya dinga azabtar da mata tare da kananan yara. Kalua ya ruda masu tsaron namun daji da ke Mirzapur amma da kyar suka kama shi daga bisani, IANS ta ruwaito.

A halin yanzu, shekarun Kalua 6 kuma an mika sa gidan namun daji da ke Kanpur inda baya saurarawa dabbobi ballantana Birai. "Mun ajiyeshi na watanni a killace kafin mu sauya masa keji," Dr. Mohammad Nasir ya sanar. "Babu wani sauyi a halin fitinarsa. A yanzu shekarunsa uku a nan amma mun yanke hukuncin zai zauna a killace har karshen rayuwarsa," yace.

Masana ilimin kula da dabbobi da suka yi aiki da Simian sun ce, Kalua ya saba shan giya amma ya ki cin kayan lambu kamar yadda sauran Birai ke yi. Sun kara da cewa halayyarsa ta dogara ne da irin yadda marikinsa ya horar da shi. A wani labari na daban, jami'in dan sanda ya harbe matashi mai shekaru 20 a duniya da ke kan babur din haya bayan ya kasa bashi N100.

Mazauna yankin sun ce, sai da dan sanda ya saita matashin mai suna Arabo Dauda sannan ya sakar masa harsashi, a wurin duba matafiya da ke garin maiha. Lamarin ya haddasa hargitsi a yankin, bayan da matasa suka fara zanga-zanga tare da barazanar kai hari ofishin 'yan sandan yankin. Har a halin yanzu ba a samu damar zantawa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ba, DSP Sulaiman Nguroje.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An yanke wa biri hukuncin ɗaurin rai da rai saboda kai wa mutane 250 hari "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?