LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bidiyo: Kyakkyawar mawakiyar Amurka da ta Musulunta, ta fara amfani da muryarta wajen rera karatun Al-Qur’aniMusulunci shine addinin da yake nunawa mutane hanya mafi dacewa. Addini ne na kowa da kowa, kowa yana da hakki akan wannan addinin, domin kuwa addini ne na dukkan duniya baki daya.

Fitacciyar mawakiya ‘yar kasar Amurka, Jennifer Grout tana daya daga cikin mutane da suka zama abin misali a Musulunci. An haifi Jennifer a Boston, ta tashi cikin addinin Kiristanci. Jennifer tana da wata baiwa ta iya waka da Larabci.

Ta fara waka a sansanin ‘yan gudun hijira na Syria, tayi karatu a Montreal kasar Canada, bayan ta kammala karatu ta koma kasar Morocco. Jennifer ita ce mawakiya ‘yar kasar Amurka ta farko da ta fara samun kyauta a wasan Larabawa na Arabs Got Talent a shekarar 2013. Tayi suna sosai a kasashen Larabawa bayan samun wannan kyauta.

Haka kuma ta cigaba da yin waka a kasashe daban-daban na duniya. Banda waka da Larabci, Jennifer ta kuma iya yin waka da yaren Andalusia, Amazigh da kuma yaren Persia.

Jennifer ta Musulunta a shekarar 2015, bayan ta hadu da saurayinta dan kasar Morocco, wanda yake shima mawaki ne. Ya samu nasarar canja mata tunani akan addinin Musulunci. A hankali ya samu ya jawo ta zuwa Musulunci ta hanyar nuna mata gaskiyar yadda Musulunci yake.

Ta ce: ‘Shine mutum mafi karfin gwiwa, juriya da kuma nuna soyayya dana sani.. Na yaba da halayensa, saboda nake so alakarmu ta cigaba da kasancewa, zaman shi Musulmi shine daya daga cikin manyan abubuwan da suka sanya na fahimci Musulunci.

“Wannan sune abubuwa mafi muhimmanci, kuma ina so na karawa kaina ilimi, domin na san ma’anar Qur’ani da Musulunci a tarihince… Na karanta a baya cewa Musulunci ba wai a baki bane ba, halayya ce take nuni da Musulunci, kuma ina ganin hakan gaskiya ne.”
A kwanakin baya wani bidiyonta ya fita wanda take karanta Amanarasulu, bidiyon ya yadu sosai a shafukan sadarwa.
                                  Jennifer Grout tana karatun Qur’ani cikin murya mai dadi

A karshe dai daga waka, Jennifer ta koma amfani da kyakkyawar muryarta wajen karanta littafi mai tsarki, wannan wata baiwa ce daga Allah. Hakan ke nuna mana Allah shine mai shiryarwa. 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


Post a comment

0 Comments