LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Iran Za Ta Mayar Da Martanin Da Ya Dace Akan Hukumar Makamashin Nukiliya Ta DuniyaWakilin Iran a hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ya bayyana cewa kasarsa za ta dauki matakin da ya dace akan hukuncin da kwamitin gwamnonin hukumar zai dauka wanda na nuna kiyayya da Iran ne.

A yau Juma’a ne wakilin na Iran Garib Abady,ya fitar da sanarwar a matsayin mayar da martani akan matakin kasashen Jamus, Birtaniya da Faransa danage da cewa Iran ta hana masu sa ido ziyartar wasu cibiyoyi a Iran.

Garib ya kara da cewa; Matakin da Kasashen na turai za su dauka ba zai sa Iran din ta kyale masu sa idon su shiga cibiyoyinta ba.

Wakilin na Iran ya ce; matakin ba shi da alaka da yanayin aiki, mataki ne na siyasa wanda babu kwarewa a cikinsa.

Bugu da kari Garib ya ce, abin takaici shi ne cewa kasashen da su ka bijiro da batun wadanda su ka mallaki makaman Nukiliya ne da wasu muggan makamai.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments