--
Yanzu-yanzu: Mutum daya ya kara mutuwa sakamakon Coronavirus

Yanzu-yanzu: Mutum daya ya kara mutuwa sakamakon Coronavirus



Wani mutumi mai shekaru 55 a duniya ya mutu a asibitin koyarwan jami'ar jihar Legas LASUTH, Idi Araba, sakamakon cutar Coronavirus. Punch ta ruwaito. A cewar Punch, Majiya a asibitin ya bayyana cewa sai bayan mutuwarsa aka gudanar da gwaji aka gano cewa yana dauke da cutar Coronavirus a jikinsa.

Yace: "An gudanar da gwajin garkuwar jiki ta alamar yatsu kuma na tabbatar da cewa yana da cutar COVID-19." Ya kara da cewa mutumin wanda ya kasance yana fama da cutar koda ya kwanta a asibitin ne ranar Alhamis. Amma masu jinyarsa suka ki bayyanawa asibitin ainihin abinda ke damunsa da kuma irin tafiye-tafiyen da yayi zuwa kasar waje a makonni baya-bayan nan sai bayan mutuwarsa. KU KARANTA: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya sakamakon Coronavirus

Majiya ya cigaba da cewa: "Mutumin bai bayyana tafiye-tafiyen da yayi ba ko kuma kila ya hadu da wani wanda yayi tafiya kasar waje ba." "Ya fadawa likitoci cewa ba ya fama tari, wahalar numfashi, ciwon gabobin jiki ko gudawa." "Amma bayan mai rijistan asibitin ya bayyana masa abubuwan da suka gano a jikinsa, mutumin ya bayyana gaskiyar cewa lallai da yiwuwan ya kamu da cutar COVID-19 saboda tafiyar da yayi kasar waje."

"Ya bayyana cewa tun lokacin da ya dawo daga kasar Holan makonni biyu da suka shude yake fama da tari." "Da aka kalubalanci yan uwansa bayan ya mutu, sun bayyana cewa lallai sun boye gaskiyar abinda yake fama da shi ne saboda suna tsoron asibitin ba zata karbeshi idan suka fadi gaskiya." Mutumin ya mutu da safen nan kuma an tafi da gawarsa.


LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Yanzu-yanzu: Mutum daya ya kara mutuwa sakamakon Coronavirus "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?