--
Covid-19: Sheikh Jingir ya yi wa Lalong biyaya, ya yi sallar Juma'a da mutane kalilan (Hotuna)

Covid-19: Sheikh Jingir ya yi wa Lalong biyaya, ya yi sallar Juma'a da mutane kalilan (Hotuna)

 Shugaban kungiyar musulunci ta Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah, JIBWIS, a jihar Plateau, Sheikh Sani Jingir, daga karshe ya yi biyaya ga dokar Gwamna Simon Lalong na hana duk wata taro na sama da mutane 50 a jihar domin kare yaduwar cutar coronavirus. Idan ba a manta ba, 

Sheikh Jingir ya yi wa daruruwan mutane limancin sallar Juma'a a masallacinsa na 'Yantaya a makon da ta gabata a ranar 27 ga watan Maris duk da dokar da gwamnatin jihar ta saka. Daga bisani, hukumar 'yan sandan farar kayan SSS sun gayyace shi ofishinsu game da saba dokar da ya yi na gwamnatin jihar a wannan lokacin da ake kokarin dakile yaduwar cutar. 

Covid-19: Sheikh Jingir ya bi umurnin Lalong, ya yi sallar Juma'a a gida Source: Facebook 

Yayin amsa tambayoyin a ofishin DSS, an ruwaito cewa an tilastawa Sheikh Jingir rubuta takardar rantsuwa ta jadadada mubaya'arsa ga gwamnatin jihar. 

A yau Juma'a, Daily Nigerian ta ruwaito cewa ba a ga Sheikh Jingir ba a harabar masallacin a lokacin sallar Juma'a inda wasu masallata da suka yi sallar su a masallacin na 'Yantaya. Wata majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa ya yi sallarsa ne a masallacin gidansa tare da mutane kalilan kamar yadda hotunan ke nuna wa. 

A baya-bayan nan dai Sheikh Jingir ya janyo cece-kuce tsakanin mutane saboda kin biyaya ga dokar gwamnatin da kuma ikirarin da ya ke yi na cewa bai amince akwai cutar coronavirus ba. An ruwaito cewa Sheikh Jingir ya yi ikirarin cewa bullar annobar ta coronavirus ba komai bane illa sharri da makirci na Yahudawa da ke kokarin dakile musulunci da musulmi. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Covid-19: Sheikh Jingir ya yi wa Lalong biyaya, ya yi sallar Juma'a da mutane kalilan (Hotuna) "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?