--
Tirkashi: Bidiyon yadda wani saurayi ya zabge wani soja da mari ya gudu saboda ya dake shi

Tirkashi: Bidiyon yadda wani saurayi ya zabge wani soja da mari ya gudu saboda ya dake shi



wannan lokaci ya nuna lokacin da wani mutumi da ba a san kowaye ba ya zabge wani soja da mari akan dukan shi da yayi.
Duk da dai ba a bayyana ainahin abinda ya saka sojan yake yi musu hukuncin ba, mutumin ya ranta ana kare yayin da sojan yaja da baya yake kokarin harbin shi da bindiga sakamakon marinsa da mutumin yayi.
Wani wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook mai suna Abdul Waris, ya sanar da cewa lamarin ya faru ne a Old Tafo cikin garin Kumasi dake kasar Ghana, a lokacin da kasashe da dama suka hana mutane fita daga gida saboda annobar Coronavirus.
Sai dai wannan din bashi da nasaba da hana fita, domin kuwa mutane da dama suna ta zirga-zirga a lokacin da lamarin ya faru.
Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance:




View this post on Instagram

A post shared by Lindaikejiblog (@lindaikejiblogofficial) on

0 Response to "Tirkashi: Bidiyon yadda wani saurayi ya zabge wani soja da mari ya gudu saboda ya dake shi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?