--

Matashiyar likita ta dakatar da aurenta don cigaba ta ceton rayuwar masu cutar covid-19

Matashiyar likita ta dakatar da aurenta don cigaba ta ceton rayuwar masu cutar covid-19



- Dakta Shifa M. Mohammed, matashiyar likita 'yar asalin kasar Indiya, ta dakatar da aurenta don ta cigaba da bawa marasa lafiya kulawa - Matashiyar likitar, mai shekaru 23, na kula da masu dauke da kwayar cutar covid-19 da aka killace a wata cibiya,

amma ta zabi kasancewa da su a kan ta tafi sha'anin aurenta - A cewar Dakta Shifa, aure zai iya jira zuwa wani lokaci na gaba, amma marasa lafiyar da take kula da su, ba zasu iya jira ba Wata matashiyar likita mai shekaru 23 a duniya da aka bayyana sunanta da Shifa M. Mohammed, ta daga ranar daurin aurenta domin ta samu natsuwa tare da tattara hankalinta a kan masu dauke da kwayar da cutar covid-19 da take kula da su. Dakta Shifa, kwararriya a bangaren tiyata, ta zabi kasancewa a wurin aikinta na kula na masu cutar coronavirus a ranar daurin aurenta, ranar 29 ga watan Maris.

Matashiyar likitar, mai shekaru 23, ta na kula da masu dauke da kwayar da cutar da aka killace ne a asibitin da take aiki; asibitin kwalejin likitanci na Pariyaram da ke garin Kannur, kamar yadda jaridar kasar Indiya, 'Hindustan Times', ta rawaito.

Dakta Shifa Source: UGC Rahoton jaridar ya bayyana cewa Dakta Shifa ta bayyana cewa aure zai iya jira, a saboda haka ta zabi bayar da lokacinta domin ceton rayuwar mutanen da cutar covid-19 ta kwantar.

Ita da kanta matashiyar likitar, ta bayyanawa manema labarai cewa, "tabbas da gaske ne, na zabi zama a wurin aikina tare da marasa lafiya da aka killace a ranar da ya kamata ta kasance ranar aurena, lamarin da yasa har wasu abokan aikina ke tsokana ta. Na fi jin dadin ceton rayuwar marasa lafiya fiye da komai."


LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
 https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Matashiyar likita ta dakatar da aurenta don cigaba ta ceton rayuwar masu cutar covid-19 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?