--
Muna iya bakin kokarin mu wajen debewa mutane kewa, amma dole zamu dakata saboda Coronavirus – Kungiyar Karuwan Najeriya

Muna iya bakin kokarin mu wajen debewa mutane kewa, amma dole zamu dakata saboda Coronavirus – Kungiyar Karuwan Najeriya



Karuwai A Najeriya sun koka akan yadda aka sanya dokar hana zirga-zirga a wasu jihohi, musamman jihar Legas da Abuja, inda suka bayyana cewa hakan ya sanya dole suka dakata da fita.



Shugabar shirye-shirye ta kungiyar karuwan ta Najeriya, Amaka Enemo, ita ce ta bayyana haka a jiya Talata, inda tace duk da suna matukar kokari wajen taimakawa al’umma amma dole za ta sanya su dakata da sana’ar tasu saboda sana’ar tasu na bukatar taba jikin mutum.


Ta kara da cewa kungiyar su ta wayar da kan mambobinta akan illar cutar ta Coronavirus.
“Akwai matsala a kasa baki daya. Mu karuwai muna iya bakin kokarin wajen debewa mutane kewa. Sai dai kuma babu wata hanya da zamu yi sana’armu ba tare da mun taba jikin mutum ba, dan haka zamu dakata na dan wani lokaci muga yadda lamarin zai kasance.
“Gwamnati ta sanya doka akan zirga-zirga, a matsayinmu na ‘yan kasa masu bin doka, ba za mu karya doka. Idan gwamnati ta ce mu zauna a gida, duka zamu bi umarni saboda babu wanda yake so ya mutu.


“Yanayin sana’armu daban ce saboda kusantar mutum da muke yi, baza ku iya hada mu da likitoci ba saboda likitoci basa kusantar mutum kamar yadda muke yi.
“Wannan doka ta shafi karuwai da kuma mutanen gida baki daya. Domin kare lafiyar mu kowa ya zauna a gida,” cewar ta.

; font-size: 18px; line-height: 30px; margin-bottom: 21px; overflow-wrap: break-word;"> Ta kara da cewa wannan doka da aka sanya za ta shafi bangaren samun kudinsu, amma dai ta san cewa ba su kadai bane masu neman kudi a kowacce rana, akwai mutane da yawa da lamarin zai shafa
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Muna iya bakin kokarin mu wajen debewa mutane kewa, amma dole zamu dakata saboda Coronavirus – Kungiyar Karuwan Najeriya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?