--
Annobar Coronavirus: Amurka ta bankado asirin nuku-nukun da kasar China ta ke yi

Annobar Coronavirus: Amurka ta bankado asirin nuku-nukun da kasar China ta ke yi



Wani rahoto da ya fito daga Jaridar Bloomberg a Ranar 1 ga Watan Afrilu ya bayyana cewa kasar Sin ta boyewa Duniya hakikanin barnar da annobar Coronavirus ta yi mata.

Hukumomin leken asirin Amurka su na zargin cewa Kasar ta Sin ba ta fadin gaskiyar adadin mutanen da cutar ta kashe. Tuni an sanar da fadar Amurka game da wannan.

Binciken Amurkan ya nuna ana zargin Sin da kin fadan gaskiyar wadanda wannan cuta ta kashe, haka zalika kasar ba ta fadin gaskiya game da wadanda su ka kamu da cutar.

Har yanzu dai rahoton wannan bincike bai shiga hannun jama’a ba, amma Bloomberg ta bayyana akwai boye-boye a alkaluman kasar Sin inda cutar COVID-19 ta fara bayyana

Alkaluman kasar Sin sun bayyana cewa mutane 82, 000 ne su ka kamu da cutar, sannan kuma mutane kimanin 3, 300 sun mutu. Amurka ta na da ja da wadannan alkaluma.

Kasar Amurka ta na fama da mutane fiye da 189, 000 da su ka kamu, bayan 4, 000 da cutar ta kashe. Gwamnatin Amurka ta dade ta na zargin Sin da kin fadawa kowa gaskiya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya na zargin Sin da jawo wannan cuta. ‘Yan majalisar jam’iyya mai mulki a Amurka, sun yi tarayya a wannan ra’ayi na sukar gwamnatin Sin.

Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, ya koka da yadda kasar Sin ta dade ta na kokawa da wannan cuta tun 2019 ba tare da sauran kasashe sun san halin da ake ciki ba.

Sai dai ana zargin sauran kasashe irinsu Amurka da kin bin matakan da ya kamata wajen hana yaduwar wannan cuta. Watakila wannan ya jawo cutar ta yi kamari fiye da Sin.

Bayan Sin, ana zargin wasu kasashen irinsu Iran, Rasha, Indonesiya, Masar da Saudi Arabia da musamman kasar Koriya ta Arewa da kin fadan gaskiyar tasirin wannan annoba.



LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Annobar Coronavirus: Amurka ta bankado asirin nuku-nukun da kasar China ta ke yi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?