--
Cutar Coronavirus ta sa za a yi wa Majalisa gibin N25b a kasafin kudin 2020

Cutar Coronavirus ta sa za a yi wa Majalisa gibin N25b a kasafin kudin 2020



Za a sake duba kasafin kudin majalisar tarayyar Najeriya na wannan shekara, inda ake tunanin gwamnatin tarayya za ta rage Naira biliyan 25.6 daga cikin kudinta.

Gwamnatin Najeriya ta dauki wannan mataki ne bayan annobar COVID-19 ta jawo rugurgujewar farashin mai a Duniya, inda mai ya rage daraja a kasuwa da fiye da 60%.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa zaftare N25 daga cikin kasafin kudin ‘Yan majalisa ya na nufin an rage 20% na kudin da ta yi tunanin batarwa a cikin shekarar bana.

Ita ma gwamnatin tarayya ta rage kasafin da ta yi na Naira tiriliyan 10.3. Yanzu abin da Najeriya ta ke sa ran kashewa a wannan shekara ra 2020 ya koma Naira tiriliyan 8.

Bayan ganin kudin gangar mai ya yi kasa a kasuwa, Najeriya ta dauki matakin cire 20% daga cikin kasafin ‘Yan majalisa da bangaren shari’a da kuma masu zartarwa.

A halin yanzu za a taba kasafin shugabanni da Ministoci da ‘Yan majalisar wakilai da na dattawa da kuma masu gudanar da shari’a. Za a sanar da majalisa wannan lamari.

‘Yan majalisar tarayya sun nuna cewa a shirye su ke su sadaukar da wani kaso na kudinsu domin Najeriya ta samu damar yakar cutar Coronavirus da ke kashe Bayin Allah.

Honarabul Muhammad Tahir Monguno ya shaidawa Jaridar cewa za a rage kasafin kudin shugabannin kasar. Za a duba a ga meya kamata a cire daga kasafin bana.

Tahir Monguno ya nuna cewa za su dakatar da batun kashe Naira biliyan 37 wajen yi wa ginin majalisa kwaskwarima. Monguno ya ce kamata ya yi ayi wani abu da kudin.
LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaappπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Cutar Coronavirus ta sa za a yi wa Majalisa gibin N25b a kasafin kudin 2020"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?