--
Annobar COVID-19: Fadar Shugaban Najeriya ta lissafo jerin kokarin Buhari

Annobar COVID-19: Fadar Shugaban Najeriya ta lissafo jerin kokarin Buhari

Fadar shugaban kasa ta bakin Femi Adesina ta jero wasu matakai da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauko a Najeriya bayan barkewar cutar Coronavirus. Ga ayyukan da shugaban kasar ya yi daga lokacin da cutar ta fara bayyana zuwa yanzu:

28 ga Junairu: Kafin shigowar cutar Najeriya, gwamnatin tarayya ta tsananta bincike a filayen tashi da saukar jirage a Najeriya da nufin gano masu cutar. 28 ga Junairu: Hukumar NCDC ta bada sanarwar da shirya wadanda za su shawo kan wannan annoba idan har cutar ta barke. 31 ga Junairu: gwamnatin tarayya ta kara shiri a daidai lokacin da WHO ta ce Najeriya ta na cikin wuraren da cutar za ta iya kamari. 27 ga Fubrairu:

Ministan lafiyan Najeriya, Dr. Osagie Ehanire, ya sanar da cewa an samu wanda ya fara shigowa da wannan cuta.

9 ga Maris: Buhari ya kaddamar da kwamiti na musamman da zai yi yaki da yaduwar COVID-19. 17 ga Maris: Gwamnatin Najeriya ta dakatar da bikin wasannin da aka shirya za a ayi a Benin, jihar Edo. 18 ga Maris: Shugaban kasa Buhari ya hana wadanda su ka fito daga wasu kasashe 13 shigowa Najeriya.

18 ga Maris: Dakatar da horaswar da ake yi wa masu yi wa kasa hidima a sansanin NYSC a fadin Najeriya. 18 ga Maris: Hukumar NFF da tsaida duk wasu wasannin kwallon kafa na makonni hudu. 18 ga Maris: Diyar shugaban kasa ta killace kanta bayan dawowa daga Ingila. 20 ga Maris: Gwamnatin Najeriya ta rufe Makarantun Sakandare da na gaba da Sakandare. 20 ga Maris: An shigar da wasu kasashen cikin sahun wadanda aka hana shigowa Najeriya.

20 ga Maris: Gwamnati ta rufe filayen sauka da tashin jiragen saman Enugu, Fatakwal da Kano. 21 ga Maris: Hukumar NRC ta dakatar da aikin jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna.

Gwamnatin Buhari ta dauki matakan takaita cutar COVID-19 a Najeriya Source: UGC 21 ga Maris: Najeriya ta rufe sauran filayen sauka da tashin jiragen Abuja da Legas. 23 ga Maris: CJN, Tanko Muhammad, ya bada umarnin a rufe kotu a Ranar 24 ga Watan Maris.

23 ga Maris: Buhari ya amince da dakatar da taron FEC da NCS a Najeriya. 23 ga Maris: Hukumar zabe na kasa INEC ta tsaida duk wasu aikinta. 24 ga Maris: Hukumar JAMB ta tsaida ayyukanta cak na tsawon makonni biyu.

24 ga Maris: Hukumar NECO ta fasa gudanar da jarrabawar shiga Makarantun Sakandaren gwamnati a fadin Najeriya. 24 ga Maris: Hukumar FCTA ta bada umarnin a rufe shaguna da kasuwanni. 24 ga Maris: Haramta sallah da zuwa coci a birnin tarayya Abuja. 25 ga Maris: An garkame filin sauka da tashin jiragen sama da ke Asaba, Delta. 27 ga Maris: An rufe iyakokin kasan Najeriya. 26 ga Maris: CBN ta bada sanarwar gudumuwar da aka fara badawa domin yaki da cutar COVID-19. 26 ga Maris: Gwamnatin tarayya ta karbi kayan tallafi daga kasar Sin.

27 ga Maris: Gwamnatin tarayya ta ba Legas Naira biliyan 10 domin yaki da annobar COVID-19. 27 ga Maris: Gwamnatin Buhari ta yabawa matakan da CBN ta dauka. An fara shirin sake duba kasafin kudin 2020. 27 ga Maris: Buhari ya bukaci Ma’aikatar kasuwanci da kungiyar MAN su fara hada magunguna da kayan abinci. 27 ga Maris: Ofishin HCSF ya fitar da jawabi, ya na umartar ma’aikata su daina zuwa ofis.

29 ga Maris: Shugaban kasa Buhari ya yi wa ‘Yan kasa jawabi a karon farko. 29 ga Maris: Shugaban kasa ya sa hannu a dokar COVID-19 na shekarar 2020. 30 ga Maris: Dokar hana fita da shugaban kasa ya sa ta fara aiki a Legas da Abuja da kwaye.

LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Annobar COVID-19: Fadar Shugaban Najeriya ta lissafo jerin kokarin Buhari "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?