--
Sakon faifan bidiyon masu dauke da covid-19 ga sauran 'yan Najeriya

Sakon faifan bidiyon masu dauke da covid-19 ga sauran 'yan Najeriya


- Wasu daga cikin masu dauke da kwayar cutar covid-19 da aka killace a jihar Legas sun aiko muhimman sako a faifan bidiyo zuwa ga sauran 'yan Najeria

- Marasa lafiyar sun shawarci 'yan Najeriya su zauna a gida, tare da yi musu gargadin cewa cutar coronavirus gaskiya ce - Kazalika, masu dauke da cutar sun mika godiya ga ma'aikatan lafiya da ke dawainiya da su tare da basu kulawa Wasu daga cikin wadanda sakamakon gwaji ya tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19,
kuma aka killcesu a asibitin cututtuka masu yaduwa (IDH) da ke Yaba a jihar Legas, sun aiko sako a ciki faifan bidiyo domin fadakar wa tare da wayar da kan sauran 'yan Najeriya a kan kwayar cutar. Kazalika, masu dauke da kwayar cutar sun mika godiyarsu ga ma'aikatan lafiya, musamman likitoci da mataimakunsu, bisa dawainiyar da suke yi da su a yayin da suke a killace.

Bidiyon masu dauke da kwayar cutar, wanda gwamnan jihar Legas, Babjide Sanwo-Olu, ya fara wallafa wa a shafinsa na tuwita, ya cigaba da zagayawa a dandalin sada zumunta a ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2020.


 A cikin faifan bidiyon, an ga masu dauke da kwayar cutar su 12 dauke da rubutattun sakonni na wayar da kan jama'a a jikin takarda suna rike da shi. Dukkansu sun yi shigar kayan kariya da takuntumin rufe baki, lamarin da yasa ba za a iya gane wadanda suka bayyana a jikin bidiyon ba.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, wata karamar yarinya, mai shekaru 8 kacal a duniya, ta bayar da gudunmawar kudin domin a yaki cutar covid-19 a Najeriya. Karamar yarinyar, Vera Akpan, 'yar asalin jihar Delta, ta fasa bankinta na ajiyar kudi tare da rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa,

Muhamnadu Buhari, domin tambayarsa a kan yadda za ta bayar da dukkan kudin ga gwamnatin tarayya. Ta bayyana cewa ta zabi bayar da kudin ne saboda bukatar kudade da gwamnati ke yi domin shawo kan annobar cutar COVID-19.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "Sakon faifan bidiyon masu dauke da covid-19 ga sauran 'yan Najeriya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?