--
An gano ta barauniyar hanyar da masu cutar coronavirus 9 suka shigo Najeriya

An gano ta barauniyar hanyar da masu cutar coronavirus 9 suka shigo Najeriya



Osagie Ehanire, ministan lafiya, ya ce mutane tara da aka samu suna dauke da kwayar cutar coronavirus a jihar Osun sun shiga Najeriya ne ta barauniyar hanya da ke kan iyakarta da kasar Benin. Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala taron kwamitin da shugaban kasa ya kafa annobar covid-19,

ministan ya bayyana cewa masu dauke da kwayar cutar sun fito ne daga kasar Kwadebuwa sannan suka bi ta cikin kasar Benin, kafin daga bisani su shigo Najeriya ta wata barauniyar hanya. Ya ce an yi nasarar datse motar da ta dauko su tare da gudanar da gwaji a kansu.

Ya bayyana cewa dukkan mutanen cikin motar, 'yan Najeriya ne da suke son dawowa bayan an rufe iyakokin kasa. Ya zuwa yanzu akwai masu dauke da kwayar cutar coronavirus guda 14 a jihar Osun, lamarin da ya saka su kasancewa jiha ta uku da ke da yawan masu dauke da kwayar cutar.

A jerin wasu sakonni da gwamnatin jihar ta fitar a shafin tuwita domin kwantar da hankalin jama'a, ta bayyana cewa, "mun san ba labari bane mai dadi cewar an samu mutane 14 da ke dauke da kwayar cutar coronavirus, amma labari mai dadi shine;

gwamnati tana yin iya bakin kokarinta domin dakile yaduwar cutar tare da tabbatar da ganin cewa masu dauke da ita sun warke." A ranar Lahadi ne gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta saka dokar rufe shige da fice tare da taron jama'a don dakile yaduwar annobar covid-19.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "An gano ta barauniyar hanyar da masu cutar coronavirus 9 suka shigo Najeriya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?