--
Magidanta sun kashe kansu da adduna akan budurwar da suka shafe shekara 2 suna so

Magidanta sun kashe kansu da adduna akan budurwar da suka shafe shekara 2 suna so




- Yankin Gilgil a kasar Kenya ya shiga rudani bayan wasu maza masu aure sun kashe kansu har lahira

- Mazan biyu sun sassari kansu da adda ne bayan sun gano mace daya suke nema na wajen shekaru biyu


- Wannan ya faru ne bayan kwanaki kadan da wani magidanci ya kusa halaka mahaucin da ke lalata da matar shi tare da bata nama kyauta Wasu masu sana'ar shanu sun yi fadan da ya kai ga har suka halaka junansu, duk kuwa a kan mace. Dukkan mazan biyu kuwa masu aure ne kuma an gano sun yi fadan ne a Ojorai da ke Gilgil a Ghana. 

Magidanta sun kashe kansu da adduna akan budurwar da suka shafe shekara 2 suna so Source: Facebook 


Masu kallo sun sha matukar mamakin yadda suka hari juna da adduna. Daya an datse shi ne a wuya da addar inda ya fadi matacce a take.

Dayan kuma ya fadi ya mutu ne a wani daji da ke da kusanci da cibiyar kiwon lafiyan garin. A yayin tattaunawa a kan aukuwar lamarin, Kwamishinan Gilgil, Ndambuki Mutheki ya ce 'yan sanda na bincikar lamarin. Ya kara da cewa ana tuhumar matar da ake zargin sun yi fada a kai. 

Wani shaida mai suna Abel Kiprokon ya bayyana cewa mazan biyu na neman matar mai yara uku ne na kusan shekaru biyu ba tare da sun sani ba. Dukkan mazan suna da aure kuma basu san juna ba har safiyar Laraba yayin da daya ya tarar da dayan yana kalaci. 

"Sun hari juna da adda," Kiprokon yace. Wannan na zuwa ne bayan rahoton wani mahaucin da ya tsallake mutuwa bayan ya ja wata mace da nama don lalata. Sa'ar shi ta kare ne bayan ya fada tarkon da mijinta ya saka mishi bayan ya gano yana lalata da matarshi. 

Bayan mijin ya samu rahoto daga makwabtan shi cewa mahaucin wanda aka fi sani da Akwai Teta, yana kwance da matarshi, sai ya dawo gida. Mijin ya tarar da Teta tare da matar shi wanda hakan yasa ya bi shi da bulala. 


Mahaucin ya gudu bayan da mijin ya shiga gida neman wani makami. Mijin ya dau alkawarin maka Teta a kotu har sai an kore shi daga garin sakamakon bibiyar matan mutane da yake. LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Magidanta sun kashe kansu da adduna akan budurwar da suka shafe shekara 2 suna so "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?