Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Monday, March 23, 2020

  Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin rufe dukkan iyakokin Najeriya

  Gwamnatin tarayya ta bada umurnin rufe dukkan iyakokin Najeriya na kasa na tsawon makonni biyu domin hana mutanen da ke dauke da cutar Coronavirus shigowa kasar. Sakataren gwamnatin tarayya wanda shine shugaban kwamiti na musamman kan lamarin Coronavirus, Boss Mustapha, ya bayyana hakan da yammacin Litinin, 23 ga Maris, 2020.

  Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki inda yace: "Bisa shawarar kwamitin yakar Coronavirus, shugaba Buhari ya bada umurnin daukan wadannan matakai: i. Dakatad da taron majalisar zantarwa har sai an bukaci hakan ii. Dage zaman masu ruwa da tsaki zuwa ranar Alhamis, 26 ga Maris, 2020 iii. Rufe dukkan iyakokin Najeriya na tsawon makonni hudu daga ranar 23 ga Maris, 2020."

  A bangare guda, mai martaba sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad ABubakar ya bada umurnin kulle dukkan Masallatan birnin tarayya Abuja.

  Hakazalika Shugabannin Masallacin kasa dake Abuja, sun sanar da dakatad da Sallolin Khamsu-Salawati da Juma'a a Masallacin tare da kulleta domin takaita yaduwar cutar Coronavirus da ta fara addaban Najeriya. A jawabin da suka saki ranar Litinin, jagorancin Masallacin sun bayyana cewa fari daga yau (23 ga Maris), za'a kulle dukkan shaguna, gidajen abinci, 

  da kasuwan dake makwabtaka da Masallacin. Jawabin yace: "Dubi ga lamarin kiwon lafiyar kasa ta COVID19, jagororin masallacin kasa ta dakatad da Khamsu-Salawati, Sallar Juma'a, tarurruka, da duk wani ayyuka a Masallacin da harabarta." "Har da Shagunan kasuwanci da gidajen abincin dake jikin Masallacin za'a kulle." "Yayinda zamu cigaba da addu'a ga Allah ya yaye mana wannan annoba kuma ya shiryar damu, muna kira da mutane su bamu hadin kai da fahita kan wannan mataki." LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin rufe dukkan iyakokin Najeriya Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI