--
Yanzun-nan: Gwamnan Zamfara ya bayar da umarnin rufe ko ina a jahar saboda coronavirus

Yanzun-nan: Gwamnan Zamfara ya bayar da umarnin rufe ko ina a jahar saboda coronavirus

- Gwamnan Zmfara, Muhammad Matawalle ya yi umurnin rufe duk wasu ofishoshi na gwamnati da ma’aikatu a fadin jahar - Hakan na daga cikin matakin da gwamnatin jahar ta dauka domin hana yaduwar cutar coronavirus

- Bincike ya nuna cewa Gwamna Bello Muhammad ya kasance a cikin gida tun bayan da ya dawo jahar a ranar Alhamis da ya gabata daga wani tafiya da ya yi zuwa kasar waje Gwamnatin jahar Zamfara ta rufe duk wasu ofishoshi na gwamnati da ma’aikatu a fadin jahar. Bincike ya nuna cewa Gwamna Bello Muhammad ya kasance a cikin gida tun bayan da ya dawo jahar a ranar Alhamis da ya gabata daga wani tafiya da ya yi zuwa kasar waje bayan ya dan yada zango a Abuja.

Gwamnan ya halarci wajen duba cibiyar killace mutane na Coronavirus a cibiyar lafiya ta tarayya, Gusau a ranar Juma’a bayan ya dawo jahar.

Uwargidar gwamnan ta Hajiya Aisha Bello Muhammad ta soke wani taron manema labarai a gidan gwamnan da misalin karfe 3:00 na rana, sa’a daya kafin lokacin da aka shirya gudanar da taron. Kwamishinan yan sandan jahar, Usman Nagoggo ya haramta duk wani taro a fadin kasar sannan ya yi umurnin rage yawan mutane a ofishishin yan sanda, ciki harda sallaman dukkanin masu kananan laifuffuka.

A wani labari makamancin haka mun ji cewa Gwamnan jahar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya sanar da rufe harkoki a jahar, inda ya kaddamar da hana zirga-zirga daga karfe 8:00 na safe zuwa 8:00 na dare. A cewar gwamnan takaita zirga-zirgan zai fara ne daga ranar Laraba kamar yadda ya sanar a ranar Litinin, 23 ya watan Maris. Ya ce akwai bukatar daukar wannan mataki sakamakon sabbin mutanen da aka samu sun kamu da cutar Coronavirus a Abuja, wanda jahar Neja ce mafi kusa da birnin tarayyar.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Yanzun-nan: Gwamnan Zamfara ya bayar da umarnin rufe ko ina a jahar saboda coronavirus "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?