--
Atiku: Gwamnan Bauchi ya yi gwaji, ya rufe kansa saboda yiwuwar yada Coronavirus

Atiku: Gwamnan Bauchi ya yi gwaji, ya rufe kansa saboda yiwuwar yada Coronavirus

Mun ji cewa akwai wadanda su ka hadu da Yaron tsohon mataimakin shugaban kasa, Muhammad Atiku Abubakar, wanda yanzu ya ke dauke da cutar COVID-19. Labari ya zo mana daga Ladan Salihu cewa Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya na cikin wadanda su ka shiga jirgi guda da Muhammad Atiku Abubakar.

Gwamnan da Tawagarsa su na tare da Yaron Atiku Abubakar ne a cikin jirgin daga Garin Legas zuwa babban birnin tarayya Abuja. Gwamnan ya ce kawo yanzu garau ya ke. Bayan isowar Alhaji Muhammad Atiku gida a Abuja ne aka fara zargin cewa ya na dauke da wannan cuta ta Coronavirus, an kuma tabbatar da haka bayan yi masa gwaji. Shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnan jihar Bauchi, Malam Ladan Salihu ya bayyana cewa babu shakka Bala Mohammed sun hadu da wannan Bawan Allah kwanaki.

Har ila yau, Salihu ya tabbatar da cewa Mai girma gwamnan ya gaisa da Muhammad Atiku Abubakar, kuma sun yi musafaha, watau sun shafa hannun juna a lokacin. Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa za a iya daukar wannan cuta yayin da aka gaisa da maras lafiya. Cutar COVID-19 ta kan dade kafin ta bayyana a jikin mutum. A halin yanzu dai Sanata Bala Mohammed ya yi gwaji domin tabbatar da halin da ya ke ciki. Sauran Mukarraban gwamnatin jihar su ma duk sun dauki wannan mataki.

Kawo yanzu dai ana ta addu’ar ganin cewa sakamakon gwajin ya nuna Gwamnan da Tawagarsa ba su kai ga kamuwa da wannan cuta da ya zagaya kasashen Duniya ba. Tsohon Mai magana da yawun baki da kuma Kwamishinan, ya shaidawa jama’a cewa Gwamna Mohammed ya killace kansa a halin yanzu, bayan aukuwar wannan lamari.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Atiku: Gwamnan Bauchi ya yi gwaji, ya rufe kansa saboda yiwuwar yada Coronavirus "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?