LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Rundunar 'yan sanda ta damke mutumin da ya kashe kwarton matarsa

- Wani mutum mai shekaru 35 mai suna Habeeb Kasali ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Ogun a kan laifin da ake zarginsa na halaka wani Bamidele Johnson 

- An kama wanda ake zargi da kisan kan ne bayan samun bayanai daga ofishin 'yan sanda na yankin Igbesa daga 'yan uwan mamacin - Bayan ganowa cewa kwarton matar shi din ya rasu, sai wanda ake zargin ya tsere. Da gaggawa kuwa DPO din ofishin 'yan sanda na Igbesa ya tura jami'ansa inda suka damko shi Wani mutum mai shekaru 35 mai suna Habeeb Kasali ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Ogun a kan laifin da ake zarginsa na halaka wani Bamidele Johnson mai shekaru 32 a duniya. 

Kasali yayi hakan ne sakamakon zargin Johnson da yake da lalata da matarsa. An kama wanda ake zargi da kisan kan ne bayan samun bayanai daga ofishin 'yan sanda na yankin Igbesa daga 'yan uwan mamacin. Kamar yadda 'yan uwan mamacin suka sanar, rikici ya sarke tsakanin wanda ake zargin da kuma mamaci a yankin Totowu. Fadan ya fara ne bayan da wanda ake zargin ya tare mamacin tare da kara ja mishi kunne a kan kwartanci da matarsa.

A wannan halin ne wanda ake zargin yayi amfani da almakashi ya sokawa mamacin sau ba adadi a kirji, ido da wuya. Hakan ne kuwa yasa mamacin ya fadi kasa rai a hannun Allah. A take aka hanzarta kai shi asibitin Crest da ke titin Isuti a Egan da ke jihar Legas inda aka tabbatar da cewa ya rasu. Bayan ganowa cewa kwarton matar shi din ya rasu, sai wanda ake zargin ya tsere. 

Da gaggawa kuwa DPO din ofishin 'yan sanda na Igbesa ya tura jami'ansa inda suka damko shi. Gawar mamacin tana babban asibitin Ota don duba musabbabin mutuwarsa. A halin yanzu, Kwamishinan 'yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson ya bada umarnin mayar da wanda ake zargin zuwa sashi na musamman na binciken manyan laifuka don bincike da gurfanarwa.


LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
Post a comment

0 Comments