--
Yanzu-yanzu: An samu mutuwan farko sakamakon Coronavirus a Najeriya - NCDC

Yanzu-yanzu: An samu mutuwan farko sakamakon Coronavirus a Najeriya - NCDC



 An samu mutum na farko da ya mutu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litinin, 23 ga Maris 2019. Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta tabbatar da mutuwar a shafinta na Tuwita. 



Jawabin ciyar yace “An samu mutuwar farko sakamakon COVID19 a Najeriya. Wani dan shekara 67 ne wanda ya dawo daga Ingila jinya.“ “Ya kasance mai fama da rashin lafiya da ciwon siga.“ Majiyarmu ta bayyana sunan mutumin matsayin, Suleiman Achigu wanda ya kasance tsohon dirakta manajan kamfanin kasuwancin man feturin Najerya PPMC. Ya mutu misalin karfe 2 na dare a asibitin koyarwan jamiar Abuja. 




Marigayin dan asalin jihar Kogi ne, kuma ya dawo daga Ingila makonni biyu da suka gabata. An ce ya fara nuna alamun cutar ranar Talata sai aka bayyanawa cibiyar NCDC inda suka dauki jininsa domin gwaji.



Da sakamakon ya fito aka tabbatar da cewa ya kamu kuma aka garzaya da shi asibitin koyarwa jamiar Abuja, Gwagwalada inda ya cika. A cewar majiya, iyalinsa sun killace kansu a cikin gida.




Mun kawo muku rahoton cewa an samu karin masu cutar Coronavirus biyar a Najeriya da safiyar yau Litinin, 23 ga Maris, 2020. Cibiyar NCDC ta tabbatar. Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita da safiyar Litinin, 23 ga Mairs misalin karfe 09:45 am. 




Daga ciki akwai haifaffen dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Jawabin yace “An tabbatar da mutane biyar da suka kamu da COVID19: 2 in Abuja, 2 a Lagos & 1 a Edo. 2 sun dawo daga kasar Ingila.“ A yanzu ga adadin masu cutar a jihohi 



Lagos- 24 


FCT- 6 Ogun- 2 Ekiti- 1 Oyo- 1 Edo- 1 Jimilla: 35 LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Yanzu-yanzu: An samu mutuwan farko sakamakon Coronavirus a Najeriya - NCDC"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?