Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Tuesday, March 10, 2020

  Wani matashi ya lakadawa kakar shi dukan tsiya saboda fasto ya ce mayya ce (Bidiyo)

  - Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta twitter mai suna samitauma ya wallafa wani bidiyo mai cike da tausayi da alhini - Bidiyon na dauke da wani mutum da ke zane kakar shi bayan fasto ya ce mishi mayya ce 

  - Mawallafin bidiyon yayi Alla-wadai da wannan jika tare da faston da ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya tarwatsasu Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta twitter mai suna samitauma ya wallafa wani bidiyo mai cike da tausayi da alhini. Bidiyon na dauke da wani mutum ne da ke zane kakar shi bayan fasto ya ce mishi mayya ce. Kamar yadda jaridar Information,ng ta ruwaito, ya fada tsohuwar da duka ne ba ji, ba gani da baukatar ta amsa laifinta. A yayin wallafa bidiyon, ya rubuta:

  “Kalla yadda wani mutum ke jibgar kakarshi bayan mugun fasto ya ce mayya ce. Ina fatan bai kashe wannan tsohuwar matar ba. Wasu fastocin suna da matsala kuma sun dage sai sun tarwatsa iyalai.”

  Ba wannan bane karo na farko da fastoci ke ire-iren hakan ga al'umma. Sannanen abu ne idan aka ce fastocin Najerya da na nahiyar Afrika sun saba cin karensu babu babbaka. 

  A kwanakin baya, Legit.ng ta ruwaito yadda wani fasto ya hada wani tafki a cikin farfajiyar cocinshi wacce ya kira da tafkin waraka. Faston nan na bari a shiga tafkin ne bayan an biya shi dubu hamsin. Ga marasa halin biyan dubu hamsin kuwa, suna biyan dubu goma don a dibar musu ruwan a gora. Faston ya sanar da mabiyan shi cewa ruwan tafkin na maganin ciwuka kuma yana yaye damuwa da talauci.   LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Wani matashi ya lakadawa kakar shi dukan tsiya saboda fasto ya ce mayya ce (Bidiyo) Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI