--
Matasan Arewa sun ba Shugaba Buhari da manyan kasa laifi kan tsige Sanusi II

Matasan Arewa sun ba Shugaba Buhari da manyan kasa laifi kan tsige Sanusi II

Shugaban kungiyar Arewa Youth Organizations ta Matasan Arewacin Najeriya, Murtala Abubakar, ya yi magana game da tsige Sarki da gwamnati ta yi a kasar Kano. Mista Murtala Abubakar ya bayyana cewa akwai laifin shugaba Muhammadu Buhari wajen wannan mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka na tunbuke Sarkin Birni. 

Jaridar Vanguard ta ce wannan kungiya ta zargi Dattawan Arewacin Najeriya da cewa ba su yi kokarin ganin sun shiga tsakanin tsohon Sarki da gwamnan Jihar Kano ba. An dauki tsawon lokaci ana samun matsala tsakanin tsohon Mai Martaba watau Malam Muhammadu Sanusi II da kuma Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje. A na sa bangaren shugaban kasa Muhammadu Buhari bai ce komai ba kusan duk tsawon wannan rikici da aka yi wanda akalla an shafe shekaru biyu ba a samun jituwa. 

Yunkurin Manyan Arewa na sasanata Gwamnatin Kano da Sanusi II bai yi aiki ba Source: UGC “Da ace shugabannin Arewa sun sa baki da tuni an manta da kawo karshen rikicin da ya ki ci - ya ki cinyewa tsakanin Muhammadu Sanusi II da aka tunbuke da kuma gwamna.” 

Shugaban wannan kungiya ta Matasa ya jefi manyan yankin na Arewa da kin nuna kishin al’umma. A cewar Abubakar, wannan shirun na manya bai taimakawa Yankin ba. Kungiyar ta bakin Murtala Abubakar ta ce: “A matsayinmu na shugabannin Matasa, za mu rike shugaban kasa Muhammadu Buhari da laifi idan har rikici ya barke a cikin Kano.” 

Wannan kungiya ta fito ta na cewa danyen aiki da gwamnati ta yi, ya na iya jawo tashin hankali. Haka zalika kungiyar ta ce shiru-shirun Buhari ta sa Ganduje ya tsige Sarkin. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Matasan Arewa sun ba Shugaba Buhari da manyan kasa laifi kan tsige Sanusi II "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?