--
Tube rawanin Sanusi II: Majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa 5

Tube rawanin Sanusi II: Majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa 5

- Majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa biyar na watanni shida dangane da hargitsin da aka samu a zauren majalisar 

- A dawowa zaman zauren da aka yi a yau Litinin, Abdulazeez Gafasa, kakakin majalisar ya ce, an dakatar da 'yan majalisar ne sakamakon take doka da suka yi 

- Wadanda aka dakatar sune: Garba Yau Gwarmai, Labaran Abdul Madari, Isyaku Ali Danja, Mohammed Bello da Salisu Ahmed Majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa biyar na watanni shida dangane da hargitsin da aka samu a zauren majalisar a ranar Litinin din makon jiya. 

Wannan hargitsin kuwa yayi sanadin kwace sandar majalisar. A dawowa zaman zauren da aka yi a yau Litinin, Abdulazeez Gafasa, kakakin majalisar ya ce, an dakatar da 'yan majalisar ne sakamakon take dokar da suka yi, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

'Yan majalisar da aka dakatar sun hada da: Garba Yau Gwarmai mai wakiltar mazabar Kunchi/Tsanyawa, Labaran Abdul Madari mai wakiltar mazabar Warawa, Isyaku Ali Danja mai wakiltar mazabar Gezawa, Mohammed Bello mai wakiltar mazabar Rimingado/Tofa da Salisu Ahmed Gwamgwazo mai wakiltar mazabar birnin Kano. 

Kamar yadda kakakin majalisar ya sanar, "Yan majalisar biyar an dakatar dasu ne sakamakon karantsaye da suka yi ga dokokin majalisar ta hudu wacce ta haramta kawo tsaiko da hana zaman majalisar. "Sun kawo rashin hankali da yunkurin kwace sandar majalisar don zagon kasa ga zaman majalisar na wannan lokacin," Gafasa yace. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Tube rawanin Sanusi II: Majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa 5"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?