Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com "Colour"
 • LABARAN YAU

  Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki,

  ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________
  Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views

  Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Monday, March 16, 2020

  Abinda yasa aka tsige Sarki Sanusi - Tanko Yakasai

  Alhaji Tanko Yakasai, dan siyasa a arewa kuma daya daga cikin wadanda suka kirkiro Arewa Consultative Forum, ya bayyana dalilin da ya jawo tsige rawanin tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido a ranar 9 ga watan Maris din 2020. A wata tattaunawa da aka yi da shi da jaridar Punch a ranar Lahadi, 

  Yakasai ya ce dalilin farko da yasa aka tsige rawanin sarkin shine yadda ya ke wa wanda ya nada shi sarki biyayya, wato tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso. Wanda tuni kuwa suke da tsananin rashin jituwa da Gwamnan yanzu, Abdullahi Umar Ganduje. 

  Abu na biyu kuwa da ya jawo tuge rawanin tsohon sarkin shine rashin fahimtar tsohuwar al'adar jihar Kano wanda hakan yasa yake aiki ba tare da dubanta ba. "An haifeni a Kano kuma na san al'adun masarautar. Tun da nake yaro har zuwa yau, da sarki mai ilimi da mara ilimi basu magana da yawa. Suna mutunta kalamansu. An haifa Sanusi a Kano ne amma tashin Legas ne da Kaduna. Mahaifinsa ma'aikacin gwamnati ne wanda ya kai matsayin babban sakatare. 

  "Al'adar ma'aikatan gwamnati ne balle wadanda ke aiiki a ma'aikatar lamurran kasashen waje na rashin zama a waje daya. Sarkin da farko yana rayuwa ne tare da tsohon ministan tsaro, Alhaji Inuwa Wada amma da mahaifinsa ya dawo sai suka canza shi. "Sarkin asalinsa dan Kano ne amma bai rayu da jama'ar Kano ba har sai da ya hau karagar mulkin masarautar. Wannan ne tushen matsalar." Yakasai ya sanar da Punch. 

  Alhaji Yakasai ya kara da cewa, babban dan marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ne yafi cancanta da karagar mulkin amma kuma gwamnan lokacin sai ya dora Sanusi. Kamar yadda ya ce, wani abu da ya kara tunzura gwamnan shine yawan maganar sarkin a kan komai kuma duk ra'ayoyinsa sun ci karo da ra'ayin al'adun jihar Kano din. Wannan kuwa kamar yadda ya sanar, ya biyo baya ne saboda sarkin bai tashi a cikin Kano din ba. 


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Abinda yasa aka tsige Sarki Sanusi - Tanko Yakasai Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI