Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Sunday, March 15, 2020

  Ta kore ni daga aiki don na ki yin zina da ita - Wani mutum ya yi korafi  - Wani mutum mai suna Penjamin Franklin ya yi korafi kan yadda shugaban wurin aikinsu ta sallame shi

  - Ma'abocin amfani da shafin Twitter ya ce hakan ta faru da shi domin a baya ya ki amince ya yi zina da shugaban wurin aikin su
  - Penjamin ya ce ya tattauna da lauyoyinsa game da batun amma sun ce masa akwai bukatar ya nemo hujojji kafin su shigar da kara

  Neman shishige wa abokan aiki abu ne da ke bata wurin aiki tare da janyo matsaloli daban-daban.
  Wani mutum mai suna Penjamin Franklin ya koka kan yadda aka kafa masa kahon zuka a wurin aiki daga baya ma aka kore shi saboda kawai ya ki amincewa ya yi zina da shugaban wurin aikin su mace.

  Penjamin ya ce da farko lokacin da shugaban su ta zo kusa da shi ta yi masa radi a kunne cewa yana da kuruciya ga shi ya yi sa'a a rayuwa bai dauki abin da muhimmanci ba.
  Ya ce a lokacin da ya ke tunanin cewa lamarin ya zo karshe kuma za ta dena damunsa kawai zai aka kira shi aka bashi takardar sallama a kan cewa baya aikinsa yadda ya kamata.

  Matashin ya ce yana zuwa aiki a kan lokaci kamar yadda ya kamata kuma babu wani abinda baya gudanarwa dai-dai gwargwado game da aikinsa.

  Mutumin ya ce ya fada wa lauyansa abinda ya faru. Sai dai ya kara da cewa idan da mace ce ta yi karar cewa shugban ta na miji ya nemi ya yi lalata da ita da tuni an yarda.
  Ya ce lauyoyinsa sun ce akwai bukatar ya gabatar da gamsassun hujjoji kafin su kai batun kara a kotu.
  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Ta kore ni daga aiki don na ki yin zina da ita - Wani mutum ya yi korafi Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI