--
Tube rawanin Sanusi: Dattjan Kano sun yi wa Ganduje zazzafan martani

Tube rawanin Sanusi: Dattjan Kano sun yi wa Ganduje zazzafan martani


Kungiyar dattijan jihar Kano ta kalubalanci sauke Sanusi Lamido a matsayin sarkin Kano da Gwamnan Abdullahi Ganduje yayi. Sun kuma yi alkawarin daukar mataki a kan abinda gwamnatin jihar tayi. Idan zamu tuna, gwamnan ya fitar da takarda a ranar Litinin ta hannun sakataren gwamnatinsa, 

Usman Alhaji a kan tube rawanin sarki Muhammadu Sanusi II a kan abinda ya kwatanta da rashin da’a ga tanadin masarautar jihar Kano din. Kamar yadda sakataren gwamnatin jihar ya bayyana, sarkin baya halartar tarukan da gwamnatin ta shirya kuma ba tare da wani dalili ba. 

A takardar da shugaban majalisar dattijan Kano, Bashir Usman Tofa yasa hannu, ya kwatanta tube rawanin Sarkin da abin takaici kuma wanda aka yi ba tare da bin ka’ida ba. Shugaban ya kara da kira ga jama’ar jihar da su kwantar da hankalinsu ba tare da an tada husuma ko hatsaniya ba.


 Tube rawanin Sanusi: Dattjan Kano sun yi wa Ganduje zazzafan martani Source: Twitter 

“Mu dattijan Kano mun fada tsananin damuwa da fargabar takardar da sakataren gwamnatin jihar kano ya karanta mai bayyana tube rawanin Mai martaba, Muhammadu Sanusi II a matsayin gwamnan jjihar Kano. “A sakamakon wannan abun alhinin da Gwamnan Ganduje yayi, muna kira ga Kanaawa da su kwantar da hankulansu don hargitsi ba zai samar da mafita ba. 


“Mun yarda da ikon Allah kuma zamu ci gaba da amincewa da duk abinda ya kaddara. Shi ke da mulki,” takardar ta ce. “Duk da haka, za mu kalubalanci wannan lamarin ta halastacciyar hanya. A takaice dai zamu bibiyi shari’armu da ke kalubalantar majalisar jihar Kano din karkashin Gwamnan wacce ta tumbuke sarkin,” cewar takardar.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Tube rawanin Sanusi: Dattjan Kano sun yi wa Ganduje zazzafan martani "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?