--
Martanin yan Najeriya kan tsige tsohon sarkin Kano Sanusi

Martanin yan Najeriya kan tsige tsohon sarkin Kano Sanusi

Al'umman Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakunansu a kan matakin da gwamnatin jahar Kano ta dauka na tsige sarki Muhammadu Sanusi na II. Mafi akasarin jama'a sun nuna bacin rai da bakin ciki a kan wannan lamari wanda ya afku a yau Litinin, 9 ga watan Maris. Hakan ya sa jaridar Legit.ng ta zakulo wasu daga cikin martanin da mabiya shafinta na Facebbok suka yi game da lamarin.

Martanin yan Najeriya kan tsige tsohon sarkin Kano Sanusi Source: UGC Ga martanin nasu: Nuhu Bala Ikara: "Hmmmmm ba komai rayuwa ce, dama Mulki ai baya tabbata idan ba mulkin Mahaliccin mu Allah ba, kuma ku sani Anyi masu Mulki iri iri abaya azzalumai da mutanen kirki kuma an wayi gari duk sun shude, saboda haka kaima ka sani idan yau Kaine wataran ba kaine ba, saboda haka mun barku da Allah." Hajja Bintu Muhammad: "Tun da nake ko a tarihi ban taba jin gwamna ya tsige sarki ba don mulkin su na gado ne kuma sai mutuwa ke rabasu da shi yasamo asali daga kalifinci ne, Allah ya ganarda da yan siyasar mu."

Muhammad Aliyu Alkali: "Kaico !!! Allah Ya kyauta da wanna 'yar kwarya-kwaryar juyin mulki a gargajiyance. Kai Ganduje ! Anya! Kana neman zaman lafiya ga Kanawa kuwa?" Muhammad Babayo Adamu: "Hmmmmm wallahi abin bayyi dadi ba, ya kai your excellency ai afuwa yakamata amasa akuma Kai nazari nesa..... Ya ubangiji katallafi MAI martaba kasaukake I amarin,,,,," 

Dogara Amina: "Kanawa kuma baku da wata saurin kima in dai batun sarauta ne. Sarautar mu ta zama gidan haya. Don dai ba'a canja asali. Da na temakawa zazzagawa na koma can." Aliyu Ahmad Inuwa: "Wannan baizo min da dadi ba amatsayi na na magoyin bayan APC wallahi wannan abin haushi ne tinda ba wannan ne abin da yadame muba cigaba mai dorewa muke so ba ramuwar gayya ba." Sarkin Yakin Dan-masani Safana:

 "Gwamnan kano kasani wannan shine na 2 cikin kuskurenda kake aikatawa, kuma munsan dalilin dayasa kukayimasa haka da an nemi shugaban qasa yasa baki yaqi. toh talakawa sunganoku sai mun fara farautarku one after the others the end." 

Ali Baba Kabir: "Ba,a gane gurgu akwale kwale idan yana zaune har saiya tashi. Gabduje kakiyayi yadda rayuwa zata zoma. Duniya budurwar wawa. Wawanma jahilin kauye ajira dole cikin 2 asami 1LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Martanin yan Najeriya kan tsige tsohon sarkin Kano Sanusi "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?