MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"

Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Monday, March 9, 2020

  Bidiyon lokacin da tsohon Sarkin Kano Sanusi ke yiwa al’umma ban kwana bayan tsige shi

  A yau Litinin, 9 ga watan Maris ne gwamnatin jahar Kano karkashin jagorancin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta tsige Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II. Bayan tsige shi sai jami'an tsaro suka mamaye masarautar inda suka hana shige da fice, 

  sannan daga bisani suka kama tsohon sarkin. An gano bidiyon tsohon Sarki Sanusi na II a filin jirgi inda ya ke bankwana da al'umman mahaifar tasa wacce ya yi kaura daga cikinta. A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Instagram an gano Sanusi tsaye a kofar shiga jirgin sama yana mai yiwa al'umma addu'a. 

  An kuma jiyo muryoyin wasu mutane suna yi masa fatan alkhairi, inda suke ihun "Allah ya sauke ka lafiya dan zaki." 

  Ga bidiyon a kasa: 
  View this post on Instagram

  A post shared by Anas umar (@a_u_kano_tunbingiwa) on

  Sakataren gwamnatin jahar Kano, Usman Alhaj ya sanar da amincewar gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ga tsige Malam Muhammadu Sunusi a matsayin sarkin Kano. Zuwa yanzu Gwamna Ganduje ya nada tsohon Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin masarautar Kano, bayan manyan fadawan masarautar masu nada Sarki sun mika sunan Aminun. A halin da ake ciki, 

  mun ji cewa biyo bayan tsige tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II mai murabus, diyarsa ta fito a kafar sadarwar zamani ta Twitter tana yin gargadi tare da kashedi ga masu jajanta musu, inji rahoton TheCables. Majiyar Legit.ng ta ruwaito diyar Malam Sunusi mai murabus, Yusrah Sunusi ta yi kira ga abokan huldarta a kafar sadarwar zamani ta Twitter da cewa su daina jajanta musu saboda ba mutuwa aka musu ba, 

  kuma basu mutu ba. Diyar Sarki mai murabus ta bayyana ma abokanta a Twitter cewa: “Ku daina turo min da ‘Innallillahi wa Inna ilayhir raji’un’ da wai ‘Muna muku jaje’ saboda ba mutuwa muka yi ba. Ta yaya ya zamo ma ni ne nake tausan abokaina, ina fada musu Ku yi hakuri. “Allah ne Ya so, Inshaa Allah hakan yaafi alheri, ku saurare ne domin kuwa zan cajeku kudin tausan da nake muku.” Inji ta. Sanin kowa ne dai Musulmai na ambaton ‘Innallillahi wa Inna ilayhir raji’un’ ne a duk lokacin da wani musifa ta fada musu, wanda yake nufin “Daga Allah mu ke, kuma zuwa gare shi zamu koma.” 


  LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Bidiyon lokacin da tsohon Sarkin Kano Sanusi ke yiwa al’umma ban kwana bayan tsige shi Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI