MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"
 • Latest News

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Monday, March 9, 2020

  Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)

  A ranar Litinin ne kafofin yada labarai da na sada zumuntar zamani suka rincabe da zancen tube rawanin Malam Muhammadu Sanusi II, sarkin Kano kashi na 14. Bayan tube rawaninsa da gwamnatin jihar Kano, 

  karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tayi, tuni jami'an tsaro suka mamaye harabar fadar sarkin Kano din. 
  Babu jimawa suka fitar dashi sannan aka nuf jihar Nasarawa da tsohon Sarkin. Ana tsammanin tubabben sarkin zai kare rayuwarsa ne a kauyen Loko da ke karamar hukumar Nasarawa da ke jihar Nasarawan Najeriya. 


  Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna) Source: Twitter Bayan aukuwar lamarin, kungiyar dattijan Kano karkashin shugabanci Bashir Tofa sun yi Alla-wadai da lamarin. Sun bayyana cewa komai kaddara ce kuma zasu ci gaba da karbar kaddarar Ubangiji. Amma tabbas lamarin ya matukar gigitasu da basu tsananin mamaki. 

  Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna) Source: Twitter Daga nan ne suka yi kira ga jama'ar Kano a kan su kwanatar da hankulansu tare da gujewa kowacce husuma ko tasin-tashina don kalubalantar lamarin. Kungiyara dattajina ta tabbatar da cewa ba za ta yi kasa a guiwa ba, sai ta garzaya gaban kotu don kalubantar lamarin ta halastacciyar hanya 

  Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna) Source: Twitter A takardar da shugaban majalisar dattijan Kano, Bashir Usman Tofa yasa hannu, ya kwatanta tube rawanin Sarkin da abin takaici kuma wanda aka yi ba tare da bin ka’ida ba. 


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI