MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"
 • Latest News

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Tuesday, March 10, 2020

  Yanzun-nan: Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya yi jawabi mai taba zuciya bayan tsige shi daga kujerarsa

  Tsigaggen sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, ya yi furucinsa na farko bayan tsige shi daga kan kujerar sarauta. Tsohon sarkin na Kano, ya nuna godiya ga Allah a kan wannan kaddara da ta same shi, sannan ya yi kira ga al’umma das u zauna lafiya sannan su yi wa sabon sarki biyayya. Ya ce:“A kullun muna cikin godiya ga Allah S.W.T, a cikin ni’imominsa wadanda basa karewa,

  a cikin ni’imomin da Allah ya yi mun, Allah S.W.T ya kaddara an nada ni sarki ranar 8 ga watan Yuni, 2014, ya raya ni cikin rayuwa da lafiya. Shekara kusan shida a kan wannan gado na wannan gaado namu mai albarka. A yau Ubangiji S.W.T wana ya bani sarautar ya kaddara, ya karba. Koda yaushe muna fada cewa sarauta ajali ne da ita, kwanakin da Allah ya rubuta a kan gado kayadaddu ne, idan ranakun nan sun zo ko ana so ko ba a so sai an tafi, saboda haka mu mun karbi dukkanin abunda Allah ya yi.

  "Mun yarda, mun gode, mun yi farin ciki kuma mun san shine alkhairi a gare mu. Muna gode ma al’umman Kano a dukkanin shekarun nan irin kauna da suka nuna mana da soyayya da biyayya da addu’o’i. Muna gode ma dukkanin wadanda suka taimaka mana a cikin harkar mulki, yan majalisarmu da hakimai da suka bamu goyon baya. Muna gode ma yan uwa na zumunci wadanda suka tsaya, suka kare martabarmu da martabar gidan nan. 

  "Muna kira ga al’umma a zauna lafiya, wanda Allah ya ba wa sarauta mun umurci iyalanmu, da ‘yaýanmu, da wadanda muke da iko a kansu da duk wanda Allah ya ba wa, al’umma suka yi masa muba’ia su je su yi masa muba’ia. Su bi shi, su kare martabarsa." Kalli bidiyon a kasa:

  A baya un ji cewa tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II mai murabus ya tattara inasa inasa ya koma kauyen Loko dake cikin karamar hukumar Nassarawa ta jahar Nassarawa. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito tsohon Sarkin ya samu rakiyar hadimansa da wasu jami’an gwamnatin jahar Kano inda suka sauka a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikwe da yammacin Litinin, 9 ga watan Maris.\


  LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Yanzun-nan: Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya yi jawabi mai taba zuciya bayan tsige shi daga kujerarsa Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI