--
Yadda wani matashi ya tarwatsa kwakwalwar budurwarsa mai juna biyu

Yadda wani matashi ya tarwatsa kwakwalwar budurwarsa mai juna biyu


- Rundunar ‘yan sandan jihar Katisna ta damke wani matashi mai shekaru 27 a kan laifin kisan kai - Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan ya sanar, an zargi matashin ne da kashe budurwar shi mai shekaru 14 a duniya 


- Ya yaudareta ne zuwa wani daji inda ya shaketa tare da buga kanta da dutse sakamakon rikicin da suke na mai cikin da ke jikinta Wani matashi mai shekaru 27 mai suna Shafi’u Haruna ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan jihar Katsina bayan da aka zargesa da kashe wata karamar yarinya mai suna Hamsiya Lawal. Kamar yadda rahoton ya bayyana, 

wanda ake zargin ya kashe yarinyar ne sakamakon rashin jituwar da suka samu a kan mamallakin cikin da ke jikinta. A wata takarda da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah ya fitar, ya ce Haruna yayi ikirarin cewa yarinyar budurwarshi ce. 
Yadda wani matashi ya tarwatsa kwakwalwar budurwarsa mai juna biyu Source: Depositphotos

Wanda ake zargin ya kasheta ne a watan Disamban 2019 a kan fadan da suka yi na wanda ke da cikin jikinta. Bayan aikata laifin kisan kan, Haruna ya boye amma an kama shi ne a ranar Talatar da ta gabata. Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan ya sanar, Haruna ya yaudari yarinyar ne zuwa wani daji da ke kusa da kauyensu inda ya shaketa tare da buga mata dutse a kanta. A take kuwa kwakwalwarta ta tarwatse wanda hakan yayi sanadin mutuwarta a take. Nan ba dadewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya. 



LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Yadda wani matashi ya tarwatsa kwakwalwar budurwarsa mai juna biyu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?