--
Tsananin talauci yasa matarshi ta gujeshi ta barshi da 'ya'ya 7, sai ga Baturiya ta zo ta aure abin ta

Tsananin talauci yasa matarshi ta gujeshi ta barshi da 'ya'ya 7, sai ga Baturiya ta zo ta aure abin ta

- Wai dama Hausawa sun ce rabo na Minallahi, tsuntsu daga sama gasasshe, kamar yadda Allah ya kawo wani mutumi mata zankadediya daga kasar Canada - Ita dai wannan mata ta zo kauyen su mutumin ne a yawon da take yi na bude indo yayin da ta taso daga kasarta ta Canada, 

sai dai tana zuwa kauyen nan sai Allah ya sanya mata soyayyar wannan mutumi - Bayan yi mata bayani akan halin da yake ciki, Baturiyar ta sha alwashin daukar nauyinsa dana 'ya'yansa zuwa kasar Canada domin su cigaba da rayuwa a can Wasu hotunan biki na wata Baturiya da wani mutumi dan nahiyar Afrika wanda yake da ‘ya’ya guda bakwai ya bazu a shafukan sadarwa na yanar gizo.

Tsananin talauci yasa matarshi ta gujeshi ta barshi da 'ya'ya 7, sai ga Baturiya ta zo ta aure abin ta Source: Facebook Yadda labarin ya bayyana shine, mutumin yana da ‘ya’ya guda bakwai, ita kuma Baturiyar ta zo yawon bude ido ne Afrika. 

A cewar wani mai amfani da dandalin sada zumunta na Twitter mai suna @PH_Promoter, mutumin matar shi ta gudu ta barshi da yara guda bakwai saboda tsananin talaucin shi. 

Sai dai wani abin mamaki shine, tana guduwa sai wannan Baturiya ta ziyarci kauyen kuma ta kamu da soyayyar wannan mutumi. A karshe sun yi aure, kuma Baturiyar ta dauki nauyin daukar su duka domin tafiya da su kasar Canada su cigaba da zama a can.LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 



0 Response to "Tsananin talauci yasa matarshi ta gujeshi ta barshi da 'ya'ya 7, sai ga Baturiya ta zo ta aure abin ta "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?