--
Dangote ya yi alkawarin N200m domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a Nigeria

Dangote ya yi alkawarin N200m domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a Nigeria

Gidauniyar alhaji Aliko Dangote (ADF) tayi alkawarin ba da gudunmuwar milyan dari niyu (N200m) domin taimakawa gwamnatin tarayya wajen takaita yaduwar cutar coronavirus a Najeriya. Zuwaira Yusuf, Shugabar gidauniyar, a wani jawabi ranar Talata a Legas,

ta bayyana cewa taimakon yana daya daga cikin muhimman manufofin gidauniyar. Zuwaira tace gidauniyar ta tanadi N124m domin taimakawa asibitoci wurin gwaji, kula da kawar da cutar a hanyoyin shiga Najeriya domin tabbatar da lafiyar kasa baki daya. 

A cewarta, gidauniyar zata samar da cibiyoyin bincike kan cutar na kimanin N36m domin taimakawa gwamnati. Tace har ila yau, gidauniyar zata bada N48m domin kula da wadanda suka kamu da cutar da kuma horar da masu kiwon lafiya. Zuwaira ta laburta yadda gidauniyar Aliko Dangote ta bada N1bn akan kawar da cutar Ebola a Nahiyar Afrika a shekarun baya. 

Tace gidauniyar ta taimakawa gwamnatin Nigeria wajen kawar da cutar Ebola ta hanyar karfafa tsaron kiwon lafiyar Nigeria. 

Dangote ya yi alkawarin N200m domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a Nigeria Source: UGC 


A bangare guda, gwamnatin tarayya tana cigaba da kokarin gano fasinjoji 155 da suka hau jirgi zuwa Nigeria tare da dan kasar Italiyan da aka tabbatar yana dauke da cutar coronavirus da ya shigo kasar. 

Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire ya bayyana hakane ga manema labarai a Abuja inda yace fasinjoji 156 suka hau jirgi tare da dan kasar Italiyan. Daily Trust ta ruwaito cewa sabanin abinda ake samu daga wasu kasashe, ba’a bayyana sunan dan Italiyan mai dauke da cutar ga Jama’a ba. Ministan yace ba’a gano wasu daga cikin fasinjojin da suka hau jirgi tare da dan Italiyan ba saboda ba’a samu bayanai daga garesu ba yadda ya kamata LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 


0 Response to "Dangote ya yi alkawarin N200m domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a Nigeria "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?