Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Tuesday, March 3, 2020

  Yadda mace mai shekaru 70 ta yi wa mafarauta jagora tsirara suka shiga daji suka kashe 'yan bindiga 40 a Neja  Wata mata mai shekaru 70, a karshen makon da ya gabata ta jagoranci tawagar 'yan banga tsirara sun shiga daji sun yi maganin wasu yan bindiga da ke addabar wasu kananan hukumomi a jihar Neja inda suka lashe a ƙalla 'yan bindiga 40. 


  Bayan kashe yan bindigan an gano cewa sun kwato manyan makamai daga hannun 'yan bindigan bayan fafatawa da su kayi a karamar hukumar Zugurma Mashegu a jihar. 


  An ruwaito cewa jagorar su 'mace' ta shafa wa yan bangan wasu magungunan gargajiya a kafarsu kafin ta musu jagora suka shiga dajin na Zugurma inda ta ce su yi harbi domin 'yan bindigan da ke boye a dajin su fito. Wata majiya ta ce 'yan bindigan sun fito daga inda suka boye suna harbi amma ba su ga matan ba da 'yan bangan. 


  Yadda mace mai shekaru 70 ta yi wa mafarauta jagora tsirara suka shiga daji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja Source: Twitter 

  Hakan yasa mafarautan suka bi sahun 'yan bindigan inda suka damke a ƙalla 40 daga cikinsu yayin da wasu suka tsere kamar yadda The Nation ta ruwaito. Wani kwararar majiya daga unguwar ya ce an umurci kwanan 'yan bindigan da ya boye a kan bishiya ya sako kuma aka kama shi yayin da wasu 'yan bindigan da suka shiga cikin gari siyo katin waya da wasu kayan masarufi suma an kama su an mika wa yan sanda. 


  Mafarautan sun shaida wa wasu 'yan kauyen cewa ba su kashe shugaban yan bindigan bane saboda suna son ya bawa yan sanda bayanai kan yadda za a kamo sauran. Rundunar yan sandan jihar ba ta ce komai a kan lamarin ba yayin da wani babban ɗan sanda ya ce an tura jami'ai su tafi dajin domin bin sahun yan bindigan da nufin kamo sauran   LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI   • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Yadda mace mai shekaru 70 ta yi wa mafarauta jagora tsirara suka shiga daji suka kashe 'yan bindiga 40 a Neja Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI