Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Tuesday, March 3, 2020

  Faston Katolika ya fada hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Benuwai

  Mun samu labari cewa wani fitaccen Fasto da ke Garin Otukpo, David Echioda, ya shiga hannun Miyagun masu garkuwa da mutane a karshen makon da ya wuce. A jiya Ranar Litinin ne Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton sace wannan Bawan Allah a Garin Alan-Akpa da ke cikin karamar hukumar Otukpo a jihar Benuwai. 

  Rahotannin sun bayyana cewa an yi gaba da Faston ne a lokacin da ya ke dawowa daga Garin Utonkon a karamar hukumar Ado, inda ya halarci wani gangami. Babban malamin katolika ya gamu da wannan rashin sa’a ne a Ranar Lahadi da rana sa'ilin da wadannan ‘Yan bindiga su ka far masa kan titi yayin da ya ke tafiya. Ainihi Rabaren David Echioda mutumin Garin Oshugbudu ne a Yankin Agatu. Amma wannan Faston ya na aiki a wani coci da ke Ochobo, karamar hukumar Ohimini.

  'Yan Sanda su na bincike game da Faston da aka sace a Jihar Benuwai Source: UGC Wadanda su ka sace Shehin Malamin Mabiyan Katolika na addinin Kirista, sun dauke wayar salularsa bayan sun kama shi kamar yadda mu ka samu labari a jiya. Wani Bawan Allah ya shaidawa ‘Yan jarida cewa ‘Yan bindigan sun tursasawa wani ‘Dan acaba da tsautsayi ta rutsa da shi ya zama masu ‘Dan jagora daga motar Faston. 

  “A lokacin da ‘Dan Acaban ya ke kokarin gyara babur dinsa a daji ne ya samu ya tsare. Wannan ‘Dan Acaba ne ya dawo ya sanar da cewa wasu sun dauke Faston a hanya.” Shaidan ya bayyana cewa an sanar da Bishof Michael Apochi wannan lamari ne a Ranar. Sai dai har yanzu ‘Yan bindigan tuntubi kowa domin a biya kudin fansar sa ba. LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI   • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Faston Katolika ya fada hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Benuwai Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI