Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com "Colour"
 • LABARAN YAU

  Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki,

  ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________
  Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views

  Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Wednesday, March 4, 2020

  Yanzu Yanzu: Al’umman Damboa sun tsere yayin da yan Boko Haram ke musayar wuta da sojoji
  Rahotanni sun kawo cewa a yanzu haka Damboa, hedkwatar wata karamar hukuma a jahar Borno na karkashin harin yan ta’addan Boko Haram. Mazauna yankin sun ce yan ta’addan sun zo su da yawa da misalin karfe 6:30 na safiyar ranar Laraba, 4 ga watan Maris sanan suka fara harbi ba kakkautawa,


  jaridar TheCable ta ruwaito. Daya daga cikin mazauna yankin ya ce sama da sa’a daya, sojoji daga rundunar soji ta brigade 25 a Damboa na ta musayar wuta da yan ta’addan. “Sun zo su da yawa a motocin hilux. Mun gan su kimanin su 20 kafin muka fara gudu cikin daji,” daya daga cikin mazauna yankin da suka tsere.

  Yanzu Yanzu: Al’umman Damboa sun tsere yayin da yan Boko Haram ke musayar wuta da sojoji Source: Facebook 


  “Sun zo a rukuni biyu. Daya sun shigo ta arewacin Sambisa saan sauran ta Alagaruno. “Sojoji daga rundunar bataliya ta 25 sun zo kimanin mintuna 30 sannan har yanzu, sama da sa’a guda, suna ta musayar wuta da yan ta’addan.” Harin na zuwa ne kwana guda tal bayan yan ta’addan sun kai hari Bwalakila, wani kauye da ke makwantaka dasu a karamar hukumar Chibok. 


  Wani mazaunin kauyen ya bayyana cewa sojojin bataliya ta 117 sun dakile harin a Chibok, amma cewa sun riga da sun sace kayayyakin abinci daga wajen mazauna kauyen da suka far mawa. Sai dai ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar, Sagir Musa ba kan harin Damboa. Wani soja daga bataliyan ya bayyana cewa dakarun soji a tsaron yankin yayinda suke samun tallafi daga rundunar sojin sama.


  “An turo wani jirgin yaki daga rundunar a Maiduguri,” in ji shi. “Don haka a yanzu muna da tallafi daga rundunar sojin sama, kuma muna kora makiyan dga wajen da kuma kare yankin. Wasun su na nan har ynzu amma mun rage karfinsu a yanzu.” LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI   • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Yanzu Yanzu: Al’umman Damboa sun tsere yayin da yan Boko Haram ke musayar wuta da sojoji Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI